Yadda shugaba Xi Jinping yake ba da jagoranci ga aikin kula da lardin Qinghai
2021-03-08 13:37:58 CRI
A jiya Lahadi, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya halarci taron tantance rahoton aikin gwamnati da tawagar lardin Qinghai ta kasar ta gudanar, a gefen zama na 4 na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC ta 13, inda ya jaddada bukatar kare muhalli, da raya kauyuka, da karfafa hadin kan al’ummomi a lardin.
Lardin Qinghai, masomar manyan koguna na Yangtse, da Huanghe, da Lancang na kasar Sin ce, wuri ne da yake taka muhimmiyar rawa a kokarin tabbatar da tsaron kasar Sin a fannin rayuwar halittu. Saboda haka, shugaba Xi Jinping na kasar Sin, yayin da yake halartar taron tawagar wakilan jama’ar lardin Qinghai a wannan karo, ya ce wani babban aiki dake gaban jami’an lardin, shi ne kokarin kare muhallin halittu, don tabbatar da ci gaban al’ummar kasar Sin. Ban da wannan kuma, shugaban ya bukaci lardin Qinghai, da ya kafa wani babban wurin shakatawa na masomar manyan koguna guda 3, gami da kebe wasu yankunan kare halittu.
Kafin haka, shugaba Xi ya jagoranci wani taro, inda aka zartas da shirin aiki na kula da wurin yawon shakatawa na masomar koguna 3 a shekarar 2015. A cewar shugaban, dalilin da ya sa ake bukatar kafa tsarin nan na kebe wasu wurare a matsayin wurin shakatawa mai matsayin kasa, shi ne domin neman karfafa ayyukan kare muhallin halittu, da gina wata kasa mai kyan gani, gami da tabbatar da zaman jituwa tsakanin dan Adam da muhallin halittu.
Ban da wannan kuma, wasu shekaru 5 da suka wuce, yayin da shugaba Xi Jinping ke halartar taron tawagar wakilan jama’ar lardin Qinghai a zaman shekara-shekara na majalisar NPC na lokacin, ya taba jaddada cewa, dole ne jami’an lardin Qinghai su yi kokarin gaggauta ayyukan kawar da talauci. Daga bisani, zuwa watan Afrilun shekarar 2020, an samu kawar da talauci a dukkan gundumomi marasa karfin tattalin arziki na lardin Qinghai. Kana a ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2021, shugaba Xi Jinping ya sanar da cimma nasarar kawar da talauci a duk fadin kasar ta Sin. Sai dai shugaban ya ce, kawar da talauci ba karshen aikin raya kasa ba ne, maimakon haka, za a ci gaba da kokarin inganta zaman rayuwar jama’ar kasar.
Zuwa yanzu, wani babban aikin dake bukatar a gudanar da shi a nan kasar Sin shi ne raya yankin karkara da kauyuka. A cewar shugaba Xi, wuyar aikin ba za ta yi kasa da ta kawar da talauci a kasar ba. Saboda haka, ana bukatar daukar karin takamaiman matakai, don zamanintar da ayyukan noma, da kyautata muhallin zama da na aiki a kauyuka, gami da wadatar da manoma. Dangane da wannan jigo, shugaban ya bukaci wakilan jama’ar lardin Qinghai da su yi kokarin aiwatar da manufar raya kauyuka, don kyautata muhallin wuraren, da sanya a iya raya sana’o’i daban daban a cikin kauyukan.
Sa’an nan wani aiki na daban da shugaba Xi Jinping ya dora muhimmanci a kai, shi ne kokarin samun hadin kai tsakanin al’ummomi daban daban na kasar Sin. Da ma lardin Qinghai wani lardi ne da ake samun kabilu daban daban, wadanda suka hada da kabilar Tibet, da ta Hui, da Sala, da Mongoliya, da dai sauransu. Yayin da shugaba Xi Jinping ke halartar taron tawagar wakilan jama’ar lardin Qinghai wasu shekaru 5 da suka wuce, ya nanata bukatar baiwa wuraren da ake samun kabilu daban daban damar raya kansu, da samun ci gaban tattalin arziki mai dorewa. Ban da haka ya ce, ya kamata a yi hakuri kan bambancin da ake samu tsakanin kabilu daban daban, da girmama al’adu na al’ummomi daban daban, da sanya mutane na wadannan kabilun za su iya hadin gwiwa tare da juna cikin jituwa, da neman samun ci gaban harkokinsu tare.
A wannan karo, shugaba Xi Jinping ya sake zama tare da tawagar wakilan jama’ar lardin Qinghai, inda ya nanata bukatar taimakawa jama’ar lardin gudanar da ayyukansu daban daban, da daidaita matsalolin da suke fuskanta, da baiwa al’ummomi daban daban damar samun wadata, da sanya su hadin kai da juna a kokarin gina kasa. A cewar shugaban, kasar Sin tamkar wani babban iyali ne, wanda ya kamata a sanya dukkan mambobinsa samun damar jin dadin zaman rayuwa. (Bello Wang)