logo

HAUSA

Sin Ba Ta Son Yin Babakere, Mutunta Juna Da Hadin Kai Sune Ginshikan Makomar Huldar Sin Da Amurka

2021-03-07 19:07:29 CRI

Sin Ba Ta Son Yin Babakere, Mutunta Juna Da Hadin Kai Sune Ginshikan Makomar Huldar Sin Da Amurka_fororder_src=http_%2F%2F5b0988e595225.cdn.sohucs.com%2Fimages%2F20180822%2Fa4bae692a87d443b9a3061e144951be6.jpeg&refer=http_%2F%2F5b0988e595225.cdn.sohucs

Kwanan baya, farfesa jami’ar Harvard Joseph S. Nye Jr. ya wallafa wani bayani mai taken “Yiwuyar dalilin da zai haifar da yaki tsakanin Sin da Amurka” a shafin yanar gizo na shirin ProjectSyndicate, inda ya nazarci sauyawar karfin kasashen biyu dake iya canja huldarsu nan gaba, don yin gargadi kan Amurka cewa, kada ta nuna rashin fahimta kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, har ta yi biris da fifiko da Amurka ke da su a fannoni daban-daban, matakin da ya kara fargaba ’yan siyasa har su dauki wasu matakan da ba su dace ba kan kasar Sin.

A hakika dai, a matsayinta na kasa mai tasowa mafi gima a duniya, abin da Sin take sa gaba shi ne kawar da talauci da samun wadatar al’umma, jami’iyyar JKS mai jan rangamar mulkin kasar, tana dukufa kan bautawa al’ummar. Kuma Sin tana da mutane mafi yawa a duniya, matakin da gwamnati ke dauka na raya tattalin arziki da habaka bukatun cikin gida don kawar da talauci, ba ma kawai zai daga alkaluman GDPn ta ba ne, har ma zai baiwa kasashen duniya damammaki masu kyau. Gwamnatin kasar Sin ta tsara shirin shekaru biyar-biyar na raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma ne domin tabbatar da kawar da talauci da samun wadata da inganta zamantakewar al’ummar kasar.

A fannin al’adu kuma, al’ummar Sinawa suna nacewa ga ra’ayin Ru, wanda ya tsaya kan gudanar da harkoki bisa ladabi da wayewar kai da amincewar juna da nuna kirki. Tana bude kofarta ga kasashen waje don neman amfani juna da cin moriya tare, kuma tana iyakacin kokarinta wajen baiwa kasashe masu tasowa taimako don samun ci gaba tare. Sin ba ta da niyyar yin kama karya a duniya ko kadan.

Irin wannan kasar Sin kamar haka, na fatan hadin kai da duk wata kasa a duniya bisa tushen mutunta juna, wato mutunta ikon mulkin kasa da cikakken yankin kasa da “kasar Sin daya tak a duniya” da amincewa da “kasa daya mai tsarin mulki biyu.” Makomar huldar Sin da Amurka ta danganta da haka. (Amina Xu)