logo

HAUSA

Karya ba za ta boye nasarorin da aka cimma wajen tabbatar da hakkin dan Adam a Xinjiang ba

2021-03-07 22:26:46 CRI

Karya ba za ta boye nasarorin da aka cimma wajen tabbatar da hakkin dan Adam a Xinjiang ba_fororder_1

Kwanan nan ne kasar Amurka da sauran wasu kasashen yammacin duniya suna ta yunkurin yada jita-jita gami da shafa ma gwamnatin kasar Sin bakin fenti kan jihar Xinjiang, a wani kokari na matsawa kasar Sin lamba bisa hujjar “hakkin dan Adam”. A wajen taron manema labarai da aka shirya a ranar Lahadi, memban majalisar gudanarwar kasar Sin, wanda kuma shi ne ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi ya maida martani kan batun, inda a cewarsa, maganar da ake cewa wai ana “kisan kiyashi” a Xinjiang ba ta da gaskiya ko kadan, karya ce zalla.

Minista Wang ya tabo wani sabon littafin da wani shahararren marubucin kasar Faransa wato Maxime Vivas ya rubuta, mai taken “kawo karshen yada labaran bogi game da kabilar Uygur”, inda ya rubuta cewa, mutanen da ba su taba zuwa Xinjiang ba, su ne suka kirkiro labaran karya, da kuma ci gaba da yada jita-jita. Malam bahaushe kan ce, karya fure take ba ta ‘ya’ya. Ban da sabon littafin da wannan marubucin Faransa ya rubuta, wata tashar intanet mai zaman kanta a kasar Amurka mai suna “Grayzone” ta taba wallafa sakamakon binciken da ta yi sau da yawa, inda ta karyata jita-jitar da masu adawa da kasar Sin suke ta kokarin yadawa dangane da jihar Xinjiang bisa hakikanin alkaluman kididdiga.

Karya ba za ta boye nasarorin da aka cimma wajen tabbatar da hakkin dan Adam a Xinjiang ba_fororder_2

A cikin dukkanin karyace-karyacen da aka yi, maganar “kisan kiyashi” ya fi ba da mamaki. Amma hakikanin gaskiya ita ce, a cikin shekaru 40 da suka gabata, yawan ‘yan kabilar Uygur a Xinjiang ya ninka har sau biyu, ta yaya aka samu “kisan kiyashin” irin haka?

Har wa yau, a wajen taro karo na 46 na majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD da ake yi yanzu, akwai wakilai daga kasashe da dama wadanda suka gabatar da jawabi don goyon-bayan kasar Sin kan batun da ya shafi Xinjiang.

Bugu da kari, a nata bangaren, mai magana da yawun gwamnatin kasar Zimbabwe, wadda ta taba kai ziyara jihar Xinjiang, madam Monica Mutsvangwa ta nuna cewa, kasar Sin ta yi bakin kokarinta wajen kiyaye zaman lafiya da bunkasuwa a Xinjiang, kuma wasu kasashen yammacin duniya ba su maida hankali kan alfanun al’ummar Xinjiang ba, ainihin makasudinsu shi ne, amfani da batun hakkin dan Adam don tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin.(Murtala Zhang)