logo

HAUSA

Me ya sa kasashe 70 ke goyon bayan matsayin da Sin take dauka kan yankin Hongkong?

2021-03-06 20:44:45 CRI

 

Me ya sa kasashe 70 ke goyon bayan matsayin da Sin take dauka kan yankin Hongkong?_fororder_微信图片_20210306204403

Wakilin kasar Belarus, ya gabatar da jawabi a madadin kasashe 70, yayin taro karo na 46 na hukumar kare hakkin Bil Adama ta MDD, inda ya nanata goyon bayansu ga tsarin “kasa daya mai tsarin mulki biyu”da Sin take aiwatarwa, kuma ya ce harkokin yankin HK, harkoki ne na cikin gidan kasar Sin da bai kamata wasu su tsoma baki ciki ba. Ban da wannan kuma, sauran kasashe 20 sun gabatar da jawabai daban-daban yayin taron, inda suka bayyana goyon baya ga kasar Sin a wannan fanni. Bugu da kari, a shekarun baya-baya nan, kasashe da dama sun bayyana adawarsu ga tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin da wasu kasashen yamma ke yi.

Hongkong wani yanki ne dake karkashin jagorancin gwamnatin tsakiyar kasar Sin, duk wani shisshige cikin harkokin Honkong, tamkar tsoma baki ne cikin harkokin gidan kasar Sin, matakin da ya sabawa tsarin mulkin MDD da ka’idojin huldar kasa da kasa, da kasashen 70 ke kokarin kiyayewa ta hanyar goyon bayan kasar Sin.

A sa’i daya kuma, al’ummar duniya na goyon bayan tsarin “kasa daya mai tsarin mulki biyu” bisa halin da yankin ke ciki. Saboda a ganinsu, bayan dawowarsa hannun babban yankin kasar, Hongkong ya ci gaba a matsayinsa na wata gabar ciniki cikin ’yanci na yankin inda yake karbar harajin kwastan da kansa, karkashin goyon bayan gwanmatin tsakiya, matakin da ya baiwa duk fadin duniya damammaki mai kyau. Abin da ya shaida cewa, tsarin “kasa daya mai tsarin mulki biyu” ya kasance nagartaccen tsarin samun kwanciyar hankali da wadatar yankin cikin dogon lokaci. (Amina Xu)