Me ka sani game da taruka biyu na kasar Sin
2021-03-05 15:13:58 CRI
Yanzu haka a nan kasar Sin, in mun ambaci batun da ya fi janyo hankalin mutanen kasar, to bai wuce manyan taruka biyu, wato taron shekara shekara na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa na kasar Sin wato CPPCC da aka bude a ranar 4 ga wata, da kuma taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC da aka bude shi a ranar 5 ga wata, wadanda suke da matukar muhimmanci. Me kuka sani game da tarukan nan biyu? Shin me ya sa suke da muhimmanci? A biyo mu cikin shirinmu na Allah Daya Gari Bamban, don jin karin haske.(Lubabatu)