logo

HAUSA

An gudanar da taruka biyu na bana a wani muhimmin lokaci

2021-03-05 15:25:37 CRI

An gudanar da taruka biyu na bana a wani muhimmin lokaci_fororder_hoto

A wannan shekara ce, Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin take cika shekaru 100 da kafuwa, kuma a bana ne aka fara aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 14. Shi ya sa, taruka biyu na bana wadanda aka shirya kamar yadda aka tsara, suna ba da muhimmiyar ma’ana, kuma akwai muhimman ayyuka da dama da za a yi cikin wadannan taruka biyu na bana.

A bana, wakilai da mambobin da suka fito daga kungiyoyi, da jam’iyyu, da kabilu, da sassa daban daban na kasar Sin, za su saurari rahoton aiki na gwamanti, da daftarin shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 14, da kuma daftarin burin da ake fatan cimmawa nan da shekarar 2035 da dai sauransu. A bana, za a mai da burin JKS da fatan al’umma a matsayin burin kasar Sin, ta hanyar zartas da wasu shirye-shirye bisa dokokin kasa.

A yayin tarukan biyu da za a tattauna harkokin kasa cikin hadin gwiwa, ya kamata mu tattauna batutuwa kan halin da ake ciki, da yin hangen nesa bisa tushen shiga sabon matakin neman bunkasuwa, da aiwatar da sabbin ra’ayoyin raya kasa, da kuma kafa wani sabon tsarin neman ci gaba. A yayin da suke yin musayar ra’ayoyi, wakilai da mambobi da suka zo daga sassa daban daban na kasar Sin, wadanda suka shafi sana’o’i daban daban, za su kara wa juna sani, da koyi daga juna, da kuma daidaita ra’ayoyi na juna. A halin yanzu, kasar Sin tana cikin muhimmin lokacin samun farfadowa baki daya, wakilai da mambobi za su yi iyakacin kokarinsu wajen ba da shawarwari masu kyau, ta yadda za a inganta bunkasuwar kasa yadda ya kamata. Haka kuma, bisa jagoranci na shugaba Xi Jinping da kwamitin tsakiyar JKS, tabbas, kasar Sin za ta fara aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 14 cikin yanayi mai kyau, da kuma cimma nasarori da dama ta yadda za a yi murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS, da kuma bude wani sabon babin gina kasar Sin ta zamani mai tsarin gurguzu a dukkanin fannoni. (Maryam Yang)