logo

HAUSA

Muradun raya kasar Sin sun baiwa duniya tabbacin bunkasuwa

2021-03-05 20:47:53 CRI

 

Muradun raya kasar Sin sun baiwa duniya tabbacin bunkasuwa_fororder_微信图片_20210305204722

A yau Juma’a ne aka bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin. Rahoton ayyukan gwamnatin da aka tantance a gun taro ya girka manyan ayyukan da za a yi a shekarar 2021, da muradun da za a cimma a wa’adin shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da al’umma na 14. Wannan rahoto ya dogaro da halin da ake ciki, kuma ya yi hangen nesa, abin da ya nuna cewa, Sin tana kokarin samun bunkasuwar tattalin arzikinta, tare da ba da tabbaci ga ingancin bunkasuwa.

Sin ta tsai da shirin samun bunkasuwar GDPn ta na kashi 6% a bana, matakin da ya yi la’akari da halin da take ciki a gida da waje.

Ban da wannan kuma, saurin bunkasuwar tattalin arzikin Sin, wani ma’auni ne dake bayyana bunkasuwar Sin yadda ya kamata, matakin da ya ingiza samun bunkasuwa mai inganci.

Jami’in kamfani mai ba da shawara na duniya A.T. Kearney Wang Yu ya shaidawa manema labarai cewa, duniya za ta kara tuntubar juna a fannin tattalin arziki da ciniki tsakanin shekarar 2021 zuwa 2022, saboda ganin rarraba allurar cutar COVID-19 a duniya, Sin za ta kaucewa illar da cutar ke kawo mata, ta koma hanyar samun burinta na matsakaici da dogon wa’adi, kuma burin da take da shi na samun bunkasuwar GDP na kashi 6% yana da ma’ana matuka.

Ban da samun bunkasuwa mai dorewa, matakin da Sin take dauka na samun bunkasuwa mai inganci, yana cikin rahoton ayyukan gwamnatin. Alal misali, zurfafa kwaskwarima a wasu muhimman bangarori, da samun bunkasuwar kamfanoni, da dogaro ga kirkire-kirkire, da habaka bukatun cikin gida, da habaka bude kofa ga kasashen waje, har ma da inganta cinikayyar shige da fice, da ma kara karfin kiyaye muhalli da dai sauransu.

Alkawarin da Sin take yiwa duniya na habakawa, da inganta bude kofarta ga waje, da kara himma da gwazo wajen shiga hadin kan kasa da kasa, zai mai da kasar Sin wata nagartacciyar kasuwa ga duniya, wadda za ta kawo amfani ga duk fadin duniya.

Kazalika, alkaluman tattalin arziki, ciki hadda cinikayyar shige da fice ta watan Jarairu da Fabrairu, sun bayyana saurin bunkasuwar tattalin arzikin Sin, kamar yadda ta yi a karshen watanni uku na bara. Abin da ya nuna cewa, kamfanonin Sin na da karfi matuka wajen ingiza bunkasuwar tattalin arzikin kasar, matakin da ya sa ko shakka babu, za a cimma burin samun bunkasuwar GDPn na kashi 6% a bana.

A shekarar bara, yawan kudin dake shafar tattalin arzikin Sin ya haura triliyan 101, wanda ya kai kashi 17% na dukkan adadin duniya. Shekarar bana, shekara ce ta farko da ta aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar na bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 14, kuma Sin za ta dauki matakan da suka dace, don samun bunkasuwa mai dorewa, da inganci ba tare da wata gargada ba, matakin da zai baiwa duniya tabbaci wajen samun bunkasuwar tattalin arzikinta. (Amina Xu)