logo

HAUSA

Duniya na kimanta manyan tarukan da kasar Sin za ta gudanar

2021-03-04 19:15:36 CRI

Duniya na kimanta manyan tarukan da kasar Sin za ta gudanar_fororder_微信图片_20210304154556     Duniya na kimanta manyan tarukan da kasar Sin za ta gudanar_fororder_微信图片_20210304154602

Yayin da a yau Alhamis, ake kaddamar da taron shekara-shekara na majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ko CPPCC a takaice, da kuma taron shekara-shekara na majalissar wakilan jama’ar kasar ko NPC da za a bude a gobe Juma’a, masharhanta daga sassan duniya daban daban, na matukar kimanta wadannan taruka, duba da irin tasirin su a fannin shata taswirar ci gaban manufofin kasar Sin.

A bana dai tarukan biyu za su gudana kamar yadda ake aiwatar da su a duk shekara, sabanin bara da aka dage lokacin aiwatar da su, sakamakon bazuwar cutar numfashi ta COVID-19.

Wani yanayi na musamman da ya bambanta tarukan na bana da sauran, shi ne yadda a bana za su gudana, a gabar da kasar Sin ta cimma nasarar kakkabe kangin talauci daga dukkanin sassa, musamman ma a yankunan karkara. Sin mai yawan al’ummu da suka kai mutum biliyan 1.4, ta cimma nasarar kawar da matsanancin talauci, a wani yanayi na ba saban ba, wato yanayin da kusan ba a taba ganin makamancin sa ba a tarihin duniya.

Bahaushe kan ce “Yabon gwani ya zama dole”, a yayin taron siyasa na kasar Sin na wannan karo, ana sa ran wakilai da mambobi na majalissun biyu, za su sake nazari, tare da tsara manufofin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar Sin, musamman karkashin ajandar ci gaban nan ta shekaru biyar-biyar, wato tsakanin shekaru 2021-2025 da ma wadanda ake fatan cimmawa a dogon zango, nan da shekarar 2035. Ko shakka babu, dabarun samar da karin ci gaba da Sin ke aiwatarwa, na matukar jan hankalin sassan duniya, da masharhanta da masu fashin baki.

Da yawa daga masu tofa albarkacin bakinsu na ganin cewa, a shekaru masu zuwa, Sin za ta kara azamar ingiza salon ci gabanta, ta yadda kasuwanninta na gida da na waje za su rika karfafar juna, yayin da kasuwanninta na gida za su zamo jigon wanzar da ci gaban tattalin arziki.

Ba ko tantama, batun nasarorin da Sin ta samu wajen shawo kan cutar COVID-19, da tallafin ta ga yaki da ake ci gaba da yi da cutar, da samar da alluran rigakafi don moriyar al’ummar ta, da kuma na sauran sassan duniya, sun zamo abun misali da ake fatan ganin majalissun na Sin guda biyu sun yi tsokaci a kan su.

A hannu guda kuma, yayin da duniya ke kokarin farfadowa daga komadar tattalin arziki, Sin ta samarwa duniya wani darasi, game da hade ayyukan raya kasa da kuma na shawo kan kalubale, da matsaloli a lokaci guda.

Saura da me? Masharhanta da yawa na ganin a wannan gaba da duniya ke fuskantar tarin kalubale, kamata ya yi a sa ido kwarai, wajen nazartar dabarun kasar Sin na shawo kan matsaloli, da kuma wanzar da ci gaba. (Saminu Alhassan)

Bello