logo

HAUSA

Kamata ya yi Amurka ta fitar da sabon tsarin cinikayya da Sin

2021-03-03 20:20:53 CRI

Kamata ya yi Amurka ta fitar da sabon tsarin cinikayya da Sin_fororder_0303-sharhi-Saminu-hoto

Babban masanin tattalin arziki, na sashen lura da aikin noma na gwamnatin Amurka Seth Meyer, ya ce ya kamata Amurka ta yi duba na tsanaki, game da wasu matakai da take dauka, don gane da alakarta da kasar Sin.

Kalaman nasa na zuwa ne bayan da ofishin wakiliyar cinikayya ta Amurka ko USTR, ya sanar da fitar da wani rahoto da ya yiwa lakabi da “Ajandar cinikayya na shekarar 2021, da rahoton shekara shekara na 2020.”

Ofishin ya fitar da wannan rahoto ne a ranar 1 ga watan nan na Maris, inda a ciki aka bayyana tsare tsaren harkokin cinikayya da Amurka za ta aiwatar. Cikin rahoton, an ambaci kasar Sin sama da sau 400, inda sabuwar gwamnatin Amurka mai ci ta rika barazanar daukar mataki kan kasar Sin, bisa zargin rashin daidaiton cin gajiyar cinikayya tsakanin kasashen biyu.

Mr. Seth Meyer ya ce, bayan duba na tsanaki game da abubuwan da wannan rahoto ya kunsa, ya kamata a bukaci marubucinsa ya tambayi manoman Amurka, game da irin ribar da suke samu daga fadada noman waken soya da masara, sakamakon karin bukatar su daga kasar Sin.

Meyer ya ce, baya ga wannan riba da manoman Amurka ke samu, kamata ya yi masu tsara manufofin Amurka su karanta binciken baya bayan nan, wanda cibiyar raya cinikayya da hadin gwiwar kamfanin Rhodium suka fitar, wanda a ciki aka kiyasta cewa, idan har Amurka ta kakaba kaso 25% na haraji ga dukkanin hada hadar cinikayya da kasar Sin, ya zuwa shekarar 2025, Amurkar za ta rika yin asarar dala biliyan 190 na kiyasin GDPn ta a duk shekara.

Masannin ya kara da cewa, kamfanonin Amurka na kara zuba jari a kasar Sin, kuma ba sa fatan ganin an gudanar da manufofi da za su gurgunta salon hadin gwiwar cin moriyar juna. Kaza lika kamar yadda wancan rahoto ya nuna, idan Amurka ta rage jarin kai tsaye da take zubawa a Sin da rabi, hakan zai haifarwa Amurkawa masu zuba jari faduwar dalar Amurka biliyan 25 a duk shekara, kuma faduwar karo daya na wannan GDP na iya kaiwa darajar dalar Amurka biliyan 500.

Ko shakka babu, akwai bukatar Amurka ta samar da managarcin tsarin gudanar da cinikayya da kasar Sin, wanda zai kunshi matakan martaba dokar hada hadar tattalin arziki da cinikayya maras shinge, da shawo kan banbance-banbance, da karfafa hadin gwiwa da abokan hulda. (Saminu )