Aliyu Muhammed Ibrahim: Ina son bayar da gudummawa ta ga inganta kauna tsakanin Najeriya da China!
2021-03-02 14:21:06 CRI
Aliyu Muhammed Ibrahim, haifaffen Kaduna ne daga arewacin Najeriya, wanda ya zo karatu a wata jami’ar dake birnin Tianjin na kasar Sin a watan Afrilun shekara ta 2019. Saboda annobar COVID-19, ya koma gida Najeriya a karshen shekarar kana bai dawo ba har yanzu.
A zantawar sa da Murtala Zhang, Aliyu Muhammed Ibrahim ya ce, duk da cewa bai dade da karatu a kasar Sin ba, ya fahimci wasu al’adun mutanen kasar, kuma ya ji dadin hulda da jama’ar kasar, saboda ba sa kyamar baki, har ma suna da karamci da halayya masu kyau.
Malam Aliyu ya ce, yana fatan dawowa kasar Sin don ci gaba da karatu nan bada dadewa ba, kuma in ya gama karatun, yana son samun wani aiki da zai iya bayar da gudummawar sa ga karfafa kauna da kyakkyawar dangantaka tsakanin gida Najeriya da kasar Sin.(Murtala Zhang)