logo

HAUSA

An samu raya tattalin arzikin Sin bisa kokarin kyautata zaman rayuwar jama’a

2021-03-01 21:12:45 CRI

An samu raya tattalin arzikin Sin bisa kokarin kyautata zaman rayuwar jama’a_fororder_20210301-sharhi-Bello

Kasar Sin ta gabatar da jimillar GDP, wato darajar kudin kayayyakin da aka samar da su a cikin gida na kasar a kwanan baya, inda jimillar ta zarce Yuan triliyan 101 a shekarar 2020, tare da karuwar kashi 2.3%, idan an kwatanta da adadin da aka samu a shekarar 2019.

Ta la’akari da mummunan tasirin da cutar COVID-19 ta haifar wa tattalin arzikin duniya, wannan ci gaban tattalin arzikin da aka samu a kasar Sin ba wani abu ne mai sauki ba.

Dalilin da ya sa kasar Sin ke iya samun ci gaba, shi ne gwamnatin kasar tana dora cikakken muhimmanci kan aikin kyautata zaman rayuwar jama’a, da mai da shi tushen manufofinta. Yayin da kasar Sin ke kokarin tinkarar annobar COVID-19, ta maida ayyukan samar da guraben aikin yi, da tabbtar da ingancin rayuwar jama’a a gaban komai, inda ta samar da dimbin matakan da suka hada da rage harajin da ake karba, da samar da karin rancen kudi ga kanana da matsakaitan kamfanoni, da dai sauransu.

A dayan hannu kuma, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a kokarin farfado da tattalin arzikin duniya. Saboda kasar tana iya samar da nau’ikan kayayyaki daban daban, da jigilarsu cikin sauri, don haka kasar ta taimakawa kokarin biyan bukatu na kasashe daban daban, musamman ma a fannonin neman samun kayayyakin kandagarkin cuta, da kayayyakin masarufi, da sauran abubuwan da ake bukata a wurin aiki.

Ko da yake har yanzu babu tabbas game da aikin raya tattalin arzikin duniya, amma a nan kasar ta Sin, tattalin arziki na samun ci gaba cikin sauri, daidai kamar yadda yake kafin bullar cutar COVID-19. (Bello Wang)

Bello