logo

HAUSA

Sin na kokarin raya sabon sha’anin raya tattalin arziki

2021-03-01 14:25:46 CRI

A yayin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 13, gano sabon abin da zai sa kaimin bunkasuwar tattalin arziki yana daya daga cikin manyan ayyukan raya tattalin arziki na kasar Sin. Yadda kasar Sin ta shafe shekaru da dama a jere tana ba da gudummawar fiye da kashi 30 cikin dari a fannin raya tattalin arzikin duniya, ba ma kawai sabon sha’anin raya tattalin arziki zai sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin Sin, har ma zai kara inganta tattalin arzikin duniya.

Yadda ake sayar da waken kofi na kasar Ruwanda kai tsaye ta yanar gizo ke nan da aka gabatar a mahajar Taobao a tsakar watan Mayu na shekarar bara, wanda wasu manoman waken kofi na kasar Ruwanda suka kalla a birnin Kigali, babban birnin kasarsu. Bayan kaddamar da shirin, an sayar da dukkan waken kofin, manoman sun yi farin ciki sosai, kana mataimakiyar babban sakataren MDD kuma sakatariyar gudanarwar kwamitin kula da tattalin arikin Afirka na MDD Vera Songwe wadda ta halarci shirin, ita ma ta samu kwarin gwiwa sosai. Ta ce,

“Ana sayar da kofi da borkono da kasar Ruwanda ke samarwa a dandalin cinikayya ta yanar gizo, muna fatan za a kara samar da kayayyakin Afirka a dandalin ciniki ta yanar gizo. Hakan yana da babbar ma’ana sosai, musamman ma a yayin da cutar COVID-19 ke haifar da mummunan tasiri ga harkokin ciniki na duniya, hakan zai sa kaimi ga kasashen Afirka su samu wadata tare da kasar Sin da kuma duniya baki daya.”

Sayar da kaya kai tsaye ta yanar gizo, wani sabon tsarin cinikayya ne da aka bullo da shi a kasar Sin a shekarun baya baya nan. Bisa ga tsarin, a kan sayar da kayayyaki cikin sauri, tare da samun makudan kudade, wanda ya shaida karfin jama’ar kasar Sin wajen harkokin sayayya. A yayin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 13, harkokin sayayya sun zama babban injin bunkasa tattalin arzikin kasar Sin, kuma babbar kasuwar kasar ta samar da sabon karfin raya tattalin arziki mai inganci a kasar, kana ya samar da sabuwar dama ga raya tattalin arzikin duniya.

Wani sakamakon binciken shekara-shekara da ake yiwa kamfanoni da kungiyar ‘yan kasuwa ta kasar Jamus dake kasar Sin ta gabatar a kwanakin baya, ya nuna cewa, kamfanonin kasar Jamus dake kasar Sin sun samu farfadowa a shekarar 2020, kana suna nuna kyakkyawar fata ga makomarsu a shekarar 2021. Shugaban zartaswa mai kula da harkokin kasa da kasa na kamfanin KPMG na kasar Jamus Andreas Gulunz ya yi bayani cewa,

“Kashi 77 cikin dari na kamfanonin da aka bincika suna hasashen cewa, ayyukansu a kasar Sin za su fi na sauran kasashen duniya. Kashi 72 cikin dari na kamfanonin sun kiyasta cewa kudin sayar da kayayyakinsu a kasar Sin a shekarar 2021 zai ci gaba da karuwa.”

Hakazalika, ana samun babban ci gaba kan ciniki ta yanar gizo a kasar Sin. Kididdigar da ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta yi, ta nuna cewa, a shekarar 2019, yawan kudin shigi da fici da aka samu daga ciniki ta yanar gizo a kasar Sin, ya kai dala biliyan 203.6, wanda ya karu da kashi 6.7 cikin dari bisa na shekara ta 2018. A ganin mataimakin shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta EU dake kasar Sin Ma Xiaoli, bunkasuwar ciniki ta yanar gizo ta kasar Sin, za ta kawo babbar dama ga nahiyar Turai. Ya ce,

“Gwamnatocin kasashen Turai da dama sun shiga harkokin ciniki ta yanar gizo, kana sana’o’i daban daban su ma suna son yin amfani da damar ciniki ta yanar gizo. Domin cin gajiyar sabuwar damar da ciniki ta yanar gizo ke kawowa, wadda za ta taimaka wajen shiga sabuwar kasuwa. Kasuwar kasar Sin tana da muhimmanci sosai ga nahiyar Turai,.” (Zainab Zhang)