logo

HAUSA

Dole ne kasashen duniya su hada kai domin yaki da ta’addanci

2021-02-28 15:57:06 CRI

Dole ne kasashen duniya su hada kai domin yaki da ta’addanci_fororder_1

Harin ta’addanci ya sake faruwa a tarayyar Najeriya a sanyin safiyar Jumma’ar da ta gabata, inda ’yan bindiga suka yi awon gaba da daliban makarantar sakandaren mata da yawansu ya kai 317 dake garin Jangebe a karamar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara a yankin arewa maso yammacin kasar, yanzu haka gwamnatin jihar ta ba da umarnin rufe dukkanin makarantun kwana dake jihar, domin kandagarkin ayyukan tsageru kan dalibai.

Wannan ba karo na farko ba ne da ’yan bindiga suka kai hari kan daliban makarantun kasar dake yammacin nahiyar Afirka, a don haka al’ummun kasashen duniya sun yi fushi matuka kan harin, kuma hukumomin kasa da kasa, ciki har da MDD, musamman ma asusun tallafawa kananan yara na MDD wato UNICEF a takaice sun bayyana damuwa, da ma yin Allah wadai da kakkausar murya kan yadda ake ci gaba da kai mummunan hari kan dalibai a kasar, tare da yin kira ga wadanda ke da hannu da su gaggauta sakin yara matan, kana gwamnatin Najeriya ta dauki matakan tabbatar da ganin an saki yaran lami lafiya, da ma tsaron dukkan dalibai dake Najeriya.

Har kullum kasar Sin tana yin adawa da duk wani nau’in aikin ta’addanci, saboda kasar Sin kasa ce mai kishin zaman lafiya da darajanta kwanciyar hankali, a ko da yaushe tana sauke nauyin kiyaye zaman lafiya bisa wuyanta, daukacin kasashen duniya suna da babbar moriya mai dorewa guda daya a kan batun yaki da ta’addanci, kuma ta dauka cewa, yayin da kasashen duniya suke kokarin yaki da ta’addanci, dole ne a martaba rawar da MDD take takawa, musamman ma a martaba rawar da kwamitin sulhun MDD yake takawa, saboda ta’addanci makiyin daukacin bil Adama ne, dole ne kasa da kasa su hada kai su dauki matakai tare, domin kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannoni daban daban, alal misali, yin cudanya a bangaren samar da bayanan yaki da ta’addanci, da katse hanyar samar da kudaden da ’yan ta’adda suke bukata yayin shirya ayyukan ta’addanci, da tusa keyar masu aikata laifuffukan ta’addanci zuwa ga kasashen asalinsu.

A cikin ’yan shekarun da suka gabata, kasar Sin ta kara mai da hankali kan hadin gwiwar shiyyoyi, alal misali ta yi kokarin yaki da ta’addanci bisa tsarin APEC wato kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki a yankin Asiya da tekun Pasific, da SCO wato kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da kuma ARF wato dandalin tattaunawa na yankin ASEAN. Kana ta taba gudanar da atisayen aikin yaki da ta’addanci cikin gidan kasar, kuma ta taba shirya atisayen aikin yaki da ta’addanci tare da sauran kasashen duniya, duk wadannan sun nuna anniyar kasar Sin mai karfi ta yaki da ta’addanci.

Duk da cewa, yaki da ta’addanci yana da babbar wahala, amma muddin ko wane mutum a ko wace kasa ya yi kokari gwargwadon karfinsa, sai za a cimma burin ganin bayan ta’addanci a duk fadin duniya, ana sa ran za a cimma burin da sauri. (Jamila)