logo

HAUSA

Ko allurar rigakafi kirar kasar Sin na da inganci?

2021-02-27 17:48:26 CRI

Ko allurar rigakafi kirar kasar Sin na da inganci?_fororder_210227-allura-Bello

Kasar Sin daya ce daga cikin kasashen da aka fara gano bullar cutar COVID-19. Sai dai kasar ta samu shawo kan yaduwar cutar, ta hanyar daukar wasu ingantattun matakai, wadanda suka hada da tace dimbin jama’a don neman gano wadanda suka harbu da cutar, da killace su tare da jinyarsu, da kula da mutanen da suka taba cudanya da wadanda suka kamu da cutar ta fasahohin sadarwa na zamani, da dai sauransu. A sa’i daya, cibiyoyin nazarin kimiyya da fasaha na kasar Sin sun samar da rigakafin cutar COVID-19 iri-iri, don biyan bukatun kasar, gami da samar wa sauran kasashe rigakafin, musamman ma kasashe masu tasowa. Sai dai ko rigakafin cutar COVID-19 na kasar Sin suna da inganci?

Zhao Lijian, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya bayyana a kwanan nan cewa, kasar Sin ta riga ta samar da tallafin allurar rigakafin cutar COVID-19 ga wasu kasashe 53, kana tana sayar da allurar zuwa ga wasu kasashe 27. Saboda haka, wadannan kasashen da suka karbi allurar rigakafi ta kasar Sin suna da masaniya game da tambayar da aka yi kan ingancin rigakafin kasar Sin.

A ranar 25 ga watan da muke ciki, wani jami’in ma’aikatar raya kasa ta kasar Uzbekistan, ya ce, an yi gwaji na matakai 3 kan allurar rigakafin cutar COVID-19 na kasar Sin a kasarsa, kana sakamakon ya nuna cewa, amfanin allurar ya kai kashi 97%, yayin da tsaronta ya kai kashi 99%. A cewar jami’in, rigakafin ya kasance daya daga cikin alluran rigakafi mafi inganci da tsaro a duniya. Kana dukkan gwaje-gwajen da aka gudanar kan allurar an yi su ne bisa ma’aunin kasa da kasa, zuwa yanzu an riga an mika rahoton ga hukumar lafiya ta duniya WHO.

A kasar Pakistan, an gudanar da gwaji na matakai 3 kan allurar rigakafin cutar COVID-19 samfurin Ad5-nCoV na kasar Sin. A cewar jami’an lafiyar kasar, bayan an yi allurar rigakafin, ingancin maganin a fannin kare mutum daga kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19 mai tsanani ya kai 100%, kana a baki daya karfin magani wajen ba da kariya ga mutum ya kai kashi 74.8%.

Ban da wannan kuma, ana gudanar da aikin yi wa dimbin jama’a allurar rigakafin cutar COVID-19 a kasar Sin. Wani rahoton da hukumar kasar ta gabatar ya nuna cewa, ya zuwa ranar 9 ga watan Fabrairun da muke ciki, an riga an yi allurar rigakafi sau miliyan 40.52 a cikin kasar, kana ba a samu labarin abkuwar matsala game da allurar ba.

A cewar Zhong Nanshan, shahararren masanin ilimin aikin likitanci na kasar Sin, wasu rigakafin cutar COVID-19 guda 2 da kasar Sin ta samar an riga an yi wa dimbin jama’a allurarsu, kana a cikin mutanen, wasu 6 daga cikin dubu 100 ne suke da yiwuwar gamuwa da wasu kananan matsaloli, irinsu zazzabi, ko kuma samun ciwo a inda aka yi musu allura. Sa’an nan yuwuwar nuna wasu alamu masu tsanani ita ce kashi 1 bisa miliyan daya. Wannan kaso ba shi da yawa, idan an kwatanta da yuwuwar nuna alamu masu tsanani bayan an yi wa mutum allurar rigakafin cutar mura, wadda ta kai kashi 3 bisa miliyan daya. Wadannan alkaluman da aka samu bisa amfani da rigakafin cutar COVID-19 na kasar Sin, su ma sun shaida ingancinsu.

Game da yadda rigakafin da kasar Sin ta samar da amfani ga dakile cutar COVID-19, cibiyar hana yaduwar cututtuka ta birnin Beijing na kasar Sin ta sheda cewa, wasu kwanaki 28 bayan an yi allurar rigakafin, sama da kashi 90% daga cikin mutanen da aka yi musu allurar sun samu garkuwan jiki game da cutar. Kana a nashi bangare, Zhong Nanshan, shahararren masanin ilimin aikin likitanci na kasar Sin, ya ce bayan fara yin allurar rigakafin cutar COVID-19 a kasar Sin har zuwa yanzu, kusan watanni 8 da suka wuce, karfin garkuwan jiki game da cutar a cikin jinin wadanda aka yi musu allurar ya kai wani matsayi na kashi 90%. A cewarsa, hakan ya nuna cewa, bayan an yi wa mutum allurar rigakafi ta kasar Sin, zai samu garkuwan jiki game da cutar da zai dore har a kalla wasu watanni 6.

Dole a gwada wani abu, kafin a iya bayyana ra’ayi game da ingancinsa. An riga an gudanar da gwaje-gwaje kan allurar rigakafin cutar COVID-19 na kasar Sin a kasashe daban daban, da yin allurarsu kan dubun-dubatar mutane. Kana dukkan alkaluman da aka samu sun shaida inganci, da tsaro, da amfanin rigakafin na kasar Sin. (Bello Wang)

Bello