logo

HAUSA

“Ruhin rashin son kai” ya taimakawa Sinawa wajen cimma nasarar kawar da talauci

2021-02-26 16:34:30 CRI

A shekrun 80 na karnin da ya gabata, gwamnatin kasar Sin ta soma aiwatar da manufar yin gwagwarmayar yaki da fatara a duk fadin kasar. A yayin bunkasar tattalin arzikin kasar, kawo karshen shekarar 2012, yawan mutane masu fama da kangin talauci a nan kasar Sin ya ragu daga kusan miliyan 800 zuwa kasa da miliyan 100.

Amma wadannan mutane masu fama da kangin talauci suna zaune ne a cikin yankunan duwatsu ko na hamada, tattalin arzikin yankunan da suke zaune ma ya samu koma baya, har ta kai babu hanyoyin mota da za su iya bi domin zuwa sauran wurare. Batun yaya za a iya fitar da su daga kangin talauci, ya zama wani kalubale mai tsanani sosai a gaban gwamnati da al’ummun Sinawa.

“Ruhin rashin son kai” ya taimakawa Sinawa wajen cimma nasarar kawar da talauci_fororder_20210226-sharhi-Sanusi-hoto

A karshen shekarar 2011, gwamnatin kasar Sin ta fitar da “Manufar kawar da talauci daga yankunan kauyuka ta hanyar raya tattalin arziki tsakanin shekarar 2011 da ta 2020”, domin kokarin fitar da dukkan mutane masu fama da talauci a yankunan kauyuka daga kangin talauci, da kuma cimma burin kafa wata kyakkyawar al’umma mai matsakaiciyar wadata a kasar Sin. Sabo da haka, a shekarar 2013, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan da suke daidai da hakikanin halin da kowane mutum, ko kowane kauye, ko kowace gunduma, wadanda suke fama da kangin talauci suke ciki, domin tabbatar da ganin an aiwatar da manufar kamar yadda ya kamata.

Kaza lika, an tattara karfin nagartattun mutane daga bangarori daban daban, da kudade da kuma kayayyaki, wajen taimakawa wadannan mutane da yankuna masu fama da kangin talauci. A cikin wadannan nagartattun mutane, akwai wasu malamai da kananan jami’ai.

A yayin bikin yabawa wadanda suka bayar da matukar gudummawa ga aikin gwagwarmayar yaki da talauci cikin shekaru 8 da suka gabata, da gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta shirya jiya, gudummawar da wasu mutane suka bayar ta burge ni sosai.

“Ruhin rashin son kai” ya taimakawa Sinawa wajen cimma nasarar kawar da talauci_fororder_20210226-sharhi-Sanusi-hoto1

Mutumiyar farko ita ce, malama Zhang Guimei, wata tsohuwar malama da aka haife ta a shekarar 1957. Yau shekaru 12 da suka gabata, bayan ta yi ritaya a wata makarantar dake lardin Heilongjiang dake arewa maso gabashin kasar Sin ta ketare duk fadin kasar Sin ta je birnin Lijiang na lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin. Ta tattara kudi, ta kafa wata makarantar sakandare ta mata, inda dukkan dalibai mata na wurin suke iya samun izinin karatu ba tare da biyan kudi ko kobo daya ba. A cikin wadannan shekaru 12 da suka gabata, yawan daliban mata da suka gama karatu daga makarantar, kuma suka samu izinin shiga jami’a domin neman karin ilmi ya kai 1,804. Amma a cikin wadannan shekaru 12 da suka gabata, malama Zhang Guimei ta kamu da cututtuka fiye da 10, kamar ciwon huhu da na kwakwalwa. A ran 17 ga wata, a lokacin da take samun lambar yabo ta “Mutane masu burge al’ummun Sinawa”, ta iya hawa dandalin bikin da kanta domin karbar lambar yabo. Amma bayan kwanaki 8 kacal, halin da take ciki ya tsananta. A yayin bikin da aka shirya washe gari, ba ta iya tafiya da kanta ba, dole ne ta zauna a kujera mai taya ta karbi lambar yabo da shugaba Xi Jinping ya mika mata.

“Ruhin rashin son kai” ya taimakawa Sinawa wajen cimma nasarar kawar da talauci_fororder_20210226-sharhi-Sanusi-hoto2

Wata malamar daban ita ce, kaka Xia Sen, mai shekaru 98 da haihuwa. Ta taba yin aiki a cibiyar nazarin harkokin zamantakewar kasar Sin. Yau shekaru 40 da suka gabata, ta yi ritaya. A lokacin da take bakin aiki, tattalin arzikin kasar Sin ba shi da karfi, albashin da take samu a kowane wata bai kai kudin Sin yuan dari 1 ba. Amma ba ta kashe kudi da yawa kan abinci ko tufafi ba, ta yi amfani da kudin wajen tallafawa dalibai 182 wadanda suka fito daga gidaje masu fama da talauci. Jimillar kudin da ta tallafa musu sun kai fiye da RMB yuan miliyan 2.

Bugu da kari, wata mace daban da ta burge ni kwarai. Wannan mace ita ce Huang Wenxiu, ’yar kabilar Zhuang, wadda ta fito daga jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta, ta kuma samu digiri na biyu a jami’ar horar da malamai ta Beijing, kuma ta samu wani aikin yi a Beijing, amma ba ta yi tantama ba, ta koma garinsu ta je karamin kauyen Baini na jihar Guangxi ta kula da aikin kawar da talauci a kauyen. Amma abin bakin ciki ya faru. A ran 17 ga watan Yunin shekarar 2019 da tsakan dare, a kan hanyarta ta koma kauyen daga garin gundumar, ta gamu da bala’in ambaliyar ruwa ta rasa ranta, a lokacin da shekarunta na haihuwa suka kai 30 kacal.

“Ruhin rashin son kai” ya taimakawa Sinawa wajen cimma nasarar kawar da talauci_fororder_20210226-sharhi-Sanusi-hoto3

Bisa alkaluman da hukumar gwamnatin kasar Sin ta fitar, an ce, mutane fiye da 1800 sun rasa rayukansu a lokacin da suka yi kokarin yaki da talauci a cikin shekaru 8 da suka gabata a duk fadin kasar Sin.

A lokacin da nake hira da abokai na na Afirka, su kan tambaye ni dalilin da ya sa kasar Sin ta samu ci gaba cikin sauri haka. A ganina, ban da manufofi masu dacewa da gwamnatin kasar Sin ta tsara, da kuma aiwartawa cikin shekaru 40 da suka gabata, “ruhin rashin son kai” da galibin Sinawa suke da shi, yana da muhimmanci. Wannan ruhi, shi ma daya ne daga cikin muhimman al’adun gargajiyar kasar Sin. Sabo da haka, a lokacin da take cudanya da sauran kasashen duniya, akwai abubuwa da yawa, kamar taimakawa kasashen Tanzania da Zambia wajen shimfida layin dogo tsakanin kasashen biyu, da kuma mayar da allurar rigakafin cutar COVID-19 ta zama kayan jama’a, ta kuma samar wa sauran kasashe masu tasowa, ciki har da wasu kasashen Afirka rigakafin cikin lokaci ba tare da karbar kudi da yawa ba, dukkansu suna bayyana yadda al’ummun Sinawa suke bayar da gudummawa ga sauran mutane ba tare da son kai ba. (Sanusi Chen)