logo

HAUSA

Gwamnatin Biden Na Bin Hanyar Da Tsohuwar Gwamnati Ta Rage Mata Wajen Gudanar Da Harkokin Dake Da Nasaba Da Kasar Sin

2021-02-25 13:33:55 CRI

Gwamnatin Biden Na Bin Hanyar Da Tsohuwar Gwamnati Ta Rage Mata Wajen Gudanar Da Harkokin Dake Da Nasaba Da Kasar Sin_fororder_微信图片_20210225132119

Gwamnatin Biden ta cika wata guda da fara gudanar da ayyukanta. Amma an lura da cewa, gwamnatinsa ita ma na bin hanyar da tsohuwar gwamnati ta rage mata, kan wasu batutuwa dake da alaka da kasar Sin, ciki hadda tattalin arziki da ciniki, da batu kan tekun Nanhai, da yaki da COVID-19 da dai sauransu.

Tun farkon kama aikinsa, Biden ya yi alkawarin mai da aikin yaki da cutar COVID-19, da farfado da tattalin arzikin kasar a gaban komai, amma a hakika, yanzu Amurka tana fuskantar babban kalubale a wadannan bangarorin biyu. A halin yanzu, yawan mamata sakamakon cutar ya haura dubu 500, kuma ba a san yaushe ne za a kai ga dakile karuwar wannan adadi ba. A kwannan baya kuma, shugaban baitulmalin kasar Amurka wato FR Jerome Powell, ya fayyace cewa, babu tabbacin makomar tattalin arzikin Amurka a nan gaba.

A makon da ya gabata, an yi taruka da dama ta kafar bidiyo, ciki hadda taron ministocin tsaro na NATO, da na shugabannin G7, da taron tsaro na Munich. Amurka da Turai suna tuntubar juna, da zummar maido da huldarsu. Ban da wannan kuma, Amurka na yunkurin zama a inuwa guda da sauran kasashe don shafawa kasar Sin bakin fenti.

A hakika dai, matakin da gwamnatin Biden ke dauka ba su da bambanci da na tsohuwar gwamnati, wato yin fito-na-fito da juna. Matakin da ya bayyana cewa, ’yan siyasar Amurka na daukar matakan da ba su dace ba kan kasar Sin. Wata ma’aikaciyar “kungiyar tsaron kasar a gaban komai” ta Amurka, ta ba da bayani kwanan baya cewa, matakan da Amurka take dauka kan kasar Sin na da hadari matuka, ya kamata kasar ta yi watsi da su. (Amina Xu)