logo

HAUSA

Jami’in IFAD: Kawar da talauci da kasar Sin ta yi, babbar nasara ce a tarihi

2021-02-25 11:29:29 CRI

A cikin shekaru 8 da suka gabata, a karkashin kakkarfan jagoranci na kwamitin tsakiya na JKS, wanda shugaban kasar Xi Jinping ya zama jigonsa, kasar Sin ta fitar da mutane kusan miliyan 100 daga kangin talauci ta hanyar yaki da talauci mafi girma da karfi a duniya, haka nan ta cimma muradun kawar da talauci na ajandar samun dauwamamman ci gaba na MDD kafin shekaru 10 da aka tsara.

Kwanan baya, shugaban Ofishin Asiya da Pacific na Asusun Bunkasa Aikin Noma na Duniya (IFAD), Nigel Brett ya bayyana a cikin wata hira da wakilin babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG dake Rome na Italiya cewa, kawar da matsanancin talauci da kasar Sin ta yi wata nasara ce a tarihi, kuma babu wata kasa daban a duniya da ta taba yin hakan.

Kafin ya kama aikin shugabancin Ofishin Asiya da Pacific na IFAD, Nigel Brett ya yi aiki na tsawon shekaru 16, a matsayin manajan ayyukan kasa na Asusun, kuma yana da kwarewa sosai a fannin kawar da talauci. Ya sani, nasarar da kasar Sin ta samu wajen kawar da matsanancin talauci ba ta zo cikin sauki ba. A ganinsa, wannan nasara ce a tarihi, ya ce,

"Idan aka duba halin da ake ciki a yau, a gani na, babu wata kasa daban da ke iya cimma wannan buri cikin sauri irin haka. Game da yadda za a kimanta wannan nasara, zan iya cewa, yana da matukar muhimmanci, kuma babbar nasara ce da aka samu a tarihi. Wadannan ba alkaluma ne kawai da ya kamata a mai da hankali a kansu ba, abu mafi muhimmanci shi ne, yadda aka rage talauci cikin sauri ta hanyar da ta dace bisa manyan tsare-tsare."

Brett ya yi nazari sosai kan fasahohin da kasar Sin ta samu game da cimma nasarar kawar da talauci. A nasa ra'ayin, irin nasarar da kasar Sin ta samu sakamako ne na hadewar abubuwa masu yawa. Na farko shi ne sanya manoma da yankunan karkara, a matsayin cibiya wajen tsara manufofi, don daukar takamaiman matakai na yaki da talauci. Na biyu shi ne, mayar da hankali kan tsarin gudanarwa da yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha, a yayin da ake kokarin kawar da talauci, don inganta dabarun magance talauci. Na uku shi ne, zuba jari mai yawa kan wasu muhimman ayyukan more rayuwa, ciki har da hanyoyin karkara, ban ruwa da magudanan ruwa, da kuma tsarin sadarwa da dai sauransu, don hade fannonin samar da kayan noma da kasuwa sosai. Ya ce,

"Dalilin da ya sa kasar Sin ta samu nasarar kawar da talauci a karshe, shi ne gwamnatin kasar ta sanya manoma a muhimmin matsayi a yayin da take tsara manufofi, tana kuma mai da hankali sosai ga zuba jari a fannin kimiyya da fasaha, da kayayyakin more rayuwa, da kuma yadda aka hade fannin sayar da kaya da kasuwa. Wadannan dalilai guda uku, su aka hade wuri guda don cimma wannan gagarumar nasara. "

Daga cikin sabbin matakan rage talauci, takamaiman matakai na yaki da talauci da aka dauka, sun taka muhimmiyar rawa wajen kawar da talauci a kasar Sin gaba daya. Brett ya gabatar da cewa, a cikin ayyuka 33 da Asusun Bunkasa Aikin Noma na Duniya ya aiwatar a kasar Sin, sun kuma koyar da irin tsarin kawar da talauci na kasar.

"Wannan tsari yana da fa'idodi da yawa. Ta hanyar daukar takamaiman matakai na yaki da talauci, gwamnati ta yi nasarar tantance wane ne matalauci, da inda talaka yake, kuma me ya sa ya zama talaka, ta yadda aka kai ga tsara takamaiman manufofi dangane da hakikanin halin da ake ciki. Kasar Sin ta yi aiki mai kyau wajen daukar takamaiman matakai na yaki da talauci. Bisa wannan tsari, mun iya tabbatar da ganin ayyukan da muke gudanarwa a kasar, suna iya amfanar rukunoni mafiya rashin karfi, kuma ba wanda aka bari a baya a yayin da ake samun ci gaba, ta yadda mutanen dake zaune a wurare za su samu wadata."

Kasar Sin ta shiga Asusun Bunkasa Aikin Noma na Kasa da Kasa a shekarar 1980, shi ne kuma hukumar kudi ta kasa da kasa ta farko da ta ba da rancen fifiko ga kasar ta Sin don samun ci gaban aikin gona. Brett ya ce, fasahohin da kasar ta samu game da rage talauci na da matukar muhimmanci, kuma sun samu karbuwa sosai a duniya cikin ’yan shekarun da suka gabata.

Asusun IFAD zai ci gaba da karfafa hadin gwiwa tare da kasar Sin a nan gaba, yana kuma fatan daga matsayin hadin kai a tsakaninsa da Sin zuwa wani sabon mataki. Ya ce,

"Fasahohin da kasar Sin ta samu na kawar da talauci, na da matukar muhimmanci ga sauran kasashen duniya. Babban darasi da za mu koya daga nasarar da kasar Sin ta samu, shi ne kawar da talauci ba mafarki ne kawai ba, zai yiwu, kuma zuriyar mu za ta iya cimma nasarar hakan." (Bilkisu Xin)