logo

HAUSA

Karyar Da Kasashen Yamma Ke Kitsawa Game Da Jihar Xinjiang Ta Kasar Sin Ba Ta Samu Shiga Ba

2021-02-25 13:34:40 CRI

Karyar Da Kasashen Yamma Ke Kitsawa Game Da Jihar Xinjiang Ta Kasar Sin Ba Ta Samu Shiga Ba_fororder_微信图片_20210225093726

Shahararren marubucin litattafan nan dan kasar Faransa Maxime Vivas, ya wallafa wani sabon littafi mai taken “Kawo karshen labarun jabu kan kabilar Uygur”. A littafin ya ce, ya kai ziyara Xinjiang, ya kuma ganewa idanunsa dimbin ’yan kabilar Uygur da masallatai. A makarantu kuma, ya ga wani malami na koyar da Sinanci da harshen Uygur, kana masu dafa abinci na samar da abincin halal. Ba za a iya ganin irin wannan yanayi na Xinjiang mai kyau a Turai ba. Sabo da akwai jita-jita dake nuna cewa, an yi kisan kare dangi na Uygur a jihar, amma a hakika dai karairayi ne kawai. Idan ka ziyarci jihar Xinjiang, za ka iya ganewa da idanunka cewa, ba zai yiyuwar bullowar irin wannan laifi ba a jihar.

Kwanan baya, an yi taro mai taken “Labaran Jami’yyar JKS” ta kafar bidiyo a Xinjiang, inda darektan jami’iyyar Kurdish ta Iraki wato KKP Kawa Mahmud ya nuna cewa, a ganinsa matakin da Sin take dauka, wajen kawar da tsatsauran ra’ayi a jihar ya cimma gagarumar nasara.

Duk wadannan abubuwa sun bayyana cewa, jihar Xinjiang wuri ne mai kyau, labaran da kasashen yamma suke bayarwa kan jihar karya ce kawai da nufin shafa bakin fenti ga gwamnatin kasar Sin, don cimma nasu burin siyasa.

Kaza lika Sin na maraba da baki daga kasashen duniya su kai ziyara jihar Xinjiang. Hakan abubuwan da za su gane da idanunsu za su shaida cewa, labarun jabu da kafofin yada labaru na yammacin duniya suka yada, su kasance kamar abin dariya ne dake yaudara kansu kawai. (Amina Xu)