logo

HAUSA

Bukatar Maje Hajji Sallah

2021-02-24 20:39:32 CRI

Bukatar Maje Hajji Sallah_fororder_1

Da alamun har yanzu wasu kasashen yamma, ba su amsa kiran da WHO da sauran kasashe kamar kasar Sin suke yi, na raba alluran riga kafin annobar COVID-19 cikin sauki da adalci tsakanin kasashen duniya ba. Wannan nema ya sa, ake ta samun kwan gaba-kwan baya wajen raba alluran riga kafin COVID-19 da wasu kasashen yamma suka samar, a hannu guda kuma, suke kokarin neman mallake riga kafin.

Sai dai kamar yadda ta yi alkawari tun farko, kasar Sin ta bayyana cewa, da zarar ta kammala bincike, ta samar har aka fara amfani da shi, to, alluran riga kafin da ta sanar din, zai kasance kayan daukacin al’ummar duniya, musamman kuma, kasashe masu tasowa ne za su fara cin gajiyarsa.Kuma bisa dukkan alamu hakan ya tabbata.

Bayanai na nuna cewa, yanzu haka an yi wa a kalla shugabanni ko kusoshin gwamnatocin kasashe sama da 8 allurar riga kafin COVID-19 da Sin ta samar,baya ga jami’an lafiya da wasu rukunin mutane masu rauni, kamar tsoffi da aka yi musu alluran riga kafin na kasar Sin a kasashe daban-daban, lamarin da ke kara shaida ingancin allurar riga kafin da kamfanonin harhada magunguna na kasar Sin suka samar.

Ita ma jaridar Washington Post ta ruwaito cewa, allurar riga kafin ta kasar Sin, ta samarwa kasashe masu tasowa damar zabar irin allurar da ta dace. Wannan ya bayyana burin hadin kan Sin da kasahen duniya kan samarwa dukkanin kasashen duniya allurar. A don haka, kamata ya yi a rarraba allurar riga kafin bisa adalci ba tare da nuna bambanci ba, ta yadda za a raba ta yadda ya kamata, musamman ma ga kasashe masu tasowa. Kalaman da babban sakataren MDD da babban darektan WHO da ma bangaren kasar Sin suka dade suna yi kan batun samar da alluran riga kafin na COVID-19. Bukatar Dara dai,aka ce kasawa.

Daga cikin shugabannin kasashen da aka yi wa allurar ta kasar Sin, akwai na Turkiyya da Seychelles da Jordan da Indonesiya da Peru da Chile da sauransu. Baya ga wasu kasashen Turai da na Afirka da Asiya da suke ci gaba da karbar tallafin riga kafin COVID-19 daga kasar Sin da ma wadanda kasashen suka yi oda, don amfanin al’ummominsu. Ko yanzu kasuwa ta watse, Dan koli ya ci riba.(Ibrahim)