logo

HAUSA

Likitocin kasar Sin sun dawo garinsu daga Eritrea tare da yabon da aka nuna musu

2021-02-24 12:54:11 CRI

Likitocin kasar Sin sun dawo garinsu daga Eritrea tare da yabon da aka nuna mata_fororder_20210224-rahoto-Sanusi Chen-hoto3

A ranar 23 ga wata, tawagar likitocin kasar Sin karo na 13 ta koma garinta dake birnin Nanyang a lardin Henan na kasar Sin daga kasar Eritrea lami lafiya. A cikin watanni 17 da suka gabata, a lokacin da likitocin tawagar suka yi aiki a kasar Eritrea, sun ba da jinya ga marasa lafiya dubu 13.4 ko fiye, har ma sun yi aikin tiyata har sau 1554. Bayan barkewar cutar COVID-19 a duk duniya, likitocin ba su gudu ba, sun tsaya a bakin aikinsu a kasar Eritrea, sun bayar da gudummawa sosai wajen yakar annobar a kasar. Yanzu ga wani rahoton da abokin aikinmu Sanusi Chen ya hada mana.

Wannan tawagar likitoci tana kunshe da likitoci 18 wadanda suka kware kan cututtukan zuciya da numfashi da wasu cutuka masu tsanani. A watan Agustan shekarar 2019 ne suka shiga asibitoci 4 dake Asmara, babban birnin kasar Eritrea, inda suka gudanar da ayyukan jiyya na yau da kullum, da wasu ayyukan tiyata tare da takwarorinsu na kasar Eritrea. Bugu da kari, sun taimakawa takwarorinsu na kasar wajen nazarta ko kuma koyar musu sabbin ilmin likitanci.

Likitocin kasar Sin sun dawo garinsu daga Eritrea tare da yabon da aka nuna mata_fororder_20210224-rahoto-Sanusi Chen-hoto2

Ko da yake suna shan aiki sosai a kullum, amma wani abun da ya fi burge Ma Panfeng, shugaban tawagar shi ne, amincin da jama’ar wurin suka nuna wa likitocin kasar Sin. A idon jama’ar wurin, likitocin kasar Sin sun kware sosai kan aikin jinya. Ma Panfeng ya bayyana wani aikin tiyata da likitocin kasar Sin suka yi wa wani mutumin da aka raunata shi da kusoshi biyu a cikin kwakwalwarsa. Mr. Ma yana mai cewa, “Kusoshi biyu a cikin kwakwalwarsa. Bayan mun fitar da su, mun auna tsawonsu, wani daga cikinsu ya kai centimita 5. Dukkansu suna kusa da layin tsakiyar kwakwalwarsa, yana da hadari sosai. A kasar Sin, har ma a duk fadin duniya, ba a faya gamuwa da irin wannan hadari ba. Mun hada dukkan karfin tawagarmu mun yi aikin tiyata, mun yi nasarar fitar da wadannan kusoshi. Da ministar kiwon lafiyar kasar Eritrea ta ji wannan labari a kashegari, ta ziyarci wannan maras lafiya. Da ta ga wannan mutum ya farka ya samu sauki, ta yi farin ciki sosai. Ta nuna yabo kwarai ga tawagar likitocin kasar Sin.”

 

Ba ma kawai likitocin kasar Sin sun gudanar da ayyukan yau da kullum a cikin asibitoci ba ne, har ma sun je wasu yankunan dake nesa da birni sun yiwa jama’ar yankunan jinya kyauta, har ma sun ba su magunguna kyauta. Sakamakon haka, a cikin zuciyar jama’ar wurin, “likitocin kasar Sin” ya kasance tamkar wata kalmar dake iya ba su fatan alheri. Mr. Sun Yu wanda ya kware kan ciwon zuciya, ya bayyana cewa, “Jama’ar wurin, ban da wadanda suke zaune a birnin kasar, sun sha wahala sosai wajen neman samun magunguna. Mun tafi yankunan karkara, mun samar musu magunguna. Sabo da haka, suna maraba da zuwanmu da hannu bibbiyu. A lokacin da muke yawo a kan titi, ana gaishe mu da Sinanci ‘Ni Hao’. Wasu marasa lafiya ma su kan nuna mana godiya da Sinanci ‘Xie Xie’.”

Likitocin kasar Sin sun dawo garinsu daga Eritrea tare da yabon da aka nuna mata_fororder_20210224-rahoto-Sanusi Chen-hoto1

Har yanzu, cutar numfashi ta COVID-19, wato Korona na yaduwa a nahiyar Afirka. A bara, a lokacin da cutar ta bullo a kasar Eritrea, ko da yake likitocin kasar Sin ma ba su da isassun kayayyakin kandagarkin cutar, amma sun yi kokarin kebe wa takwarorinsu na wurin takunkumin baki da hanci. Sun kuma yi kokarin taimakawa hukumar kiwon lafiya ta kasar wajen tinkarar cutar. Mr. Ma Panfeng yana ganin cewa, “Mun ba da shawarwarin kandagarkin cutar guda 9 ga ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Eritrea. Mun kuma bayyana wa ministar kiwon lafiya fasahohin da bangaren Sin ya samu wajen tinkarar cutar. Bugu da kari, mun taimaka wa ma’aikatar kiwon lafiya wajen tabbatar da abubuwan kandagarkin cutar da kasar take fatan WHO ta samar mata cikin gaggawa. A farkon lokacin bullar cutar, gwamnatin kasar Eritrea ba ta san wadanne irin abubuwa ne take bukata ba. Mun kuma taimakawa bangaren Eritrea wajen zabar wurin gwaji na tantance cutar, har ma mun taimaka musu wajen kyautata aikin raba masu kamuwa da cutar da sauran mutane.”

Bisa shirin da aka tsara, ya kamata wadannan likitocin kasar Sin su yi aiki watanni 12, amma daga karshe dai, sun yi aiki a kasar Eritrea har na tsawon watanni 17. A ran 23 ga wata, sun dawo garinsu dake nan kasar Sin lami lafiya, sabo da wata tawagar likitocin kasar Sin ta daban ta riga ta isa, har ma ta fara aiki a kasar ta Eritrea a karshen watan Janairun bana. (Sanusi Chen)