logo

HAUSA

Adalci wajen rabon allurar riga kafin COVID-19, kare hakkin al’umma ne

2021-02-23 20:32:32 CRI

Adalci wajen rabon allurar riga kafin COVID-19, kare hakkin al’umma ne_fororder_Euz4UUCXMAIR1WU

Yayin da aka bude taron Majalisar Kare Hakkin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya a jiya, Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya jaddada bukatar tabbatar da adalci wajen rabon riga kafin cutar COVID-19 a duniya, yana mai cewa, kamata ya yi allurar riga kafin ta zama hajar da duk duniya za ta samu cikin rahusa.

Barkewar annobar COVID-19 ta kara haskaka yadda dangantakar dukkan bil adama ta ke, wato dai, dukkansu ‘yan uwan juna ne, babu bambancin launi ko kabila ko kasa, haka ma addini. Babu wani ko wata kasa da za ta bugi kirji ta ce idan ta dakile cutar a tsakanin al’ummarta, to ta kammala yaki da ita. Sai dai idan za ta ci gaba da kasancewa ita kadai ba tare da hulda da wata kasa ba, lamarin da ba za yuwu ba a wannan zamani da ake ciki na hadin kan kasa da kasa.

Adalci wajen rabon allurar riga kafin COVID-19, kare hakkin al’umma ne_fororder_download

Abin takaici ne yadda kasashe masu sukuni ke ci gaba da sayen riga kafin fiye da yadda suke bukata, yayin da galibin kasashe masu tasowa musammam a nahiyar Afrika, ba su kai ga samun alluran ba. kawo yanzu, kasashe 10 ne kadai ke da sama da kaso 75 na jimilar wadanda aka yi wa riga kafin a fadin duniya.

Kare hakkin bil adama bai tsaya kan karesu daga tozarci ko bambamci ba, kiwon lafiya babban hakki ne da ya rataya akan gwamnatocin duniya. Ya kamata a yi la’akari da mummunan yanayin da annobar COVID-19 ta jefa daukacin al’ummar duniya wajen tabbatar da kowa ya samu riga kafin domin dakile cutar baki daya. Kamar yadda Sakatare Janar din ya bayyana, annobar ta kara ta’azzara matsalolin da dama can dan adam ake fama da su.

Tun ma kafin kammala samar da alluran, kasar Sin ta yi alkawarin samar da shi cikin rahusa ga duk duniya musammam kasashen masu tasowa, ciki har da nahiyar Afrika, kuma tuni ta fara cika wannan alkawari da ta dauka duk da cewa, ita ma tana bukatar allurar. Irin wannan sadaukarwa da kauna da kuma tausayi da sanin ya kamata, ake bukata daga manyan kasashen duniya domin a gudu tare a tsira tare. Gazawa wajen tabbatar da adalci a yunkurin yi wa jama’a riga kafin ba zai taba haifar da da mai ido ba, kana ba za a samu nasarar dakile cutar kamar yadda ake fata ba. (Fa’iza Mustapha)