logo

HAUSA

Me ya sa munanan masifu sake faruwa a Amurka?

2021-02-23 20:51:14 CRI

Me ya sa munanan masifu sake faruwa a Amurka?_fororder_1

Ya zuwa jiya 22 ga wata, gaba daya adadin mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da annobar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Amurka ya zarta dubu 500, adadin da ya dara sojojin kasar da suka mutu yayin yakin duniya na farko da na biyu da kuma yakin Vietnam yawa, babban masanin cututtuka masu yaduwa na Amurka Anthony S. Fauci ya kira lamarin da babban abin tsoro a tarihin kasar.

Me ya sa munanan masifu sake faruwa a Amurka?_fororder_3

Haka kuma, yayin mahaukaciyar guguwar da ta aukawa jihar Texas ta kasar Amurka, mutanen da suka rasu sakamakon tsananin sanyi sun kai 76, an ga mazauna jihar wadanda suka tsira daga cutar COVID-19 sun gamu da ajalinsu a cikin dakuna ko motoci ko farfajiyar gidajensu, a ciki, akwai yara kanana. Jarihar New York Times ta wallafa wani rahoto, inda aka bayyana cewa, wata wuka mai kaifi ta huda sansanin samar da man fetur da iskar gas mafi girma a Amurka, inda miliyoyin mutane suke rayuwa cikin sanyi da dubu.

Mutane dubu 500 da 76, sun nuna cewa, al’ummun Amurka suna fuskantar kalubale mai tsanani, sakamakon annoba da masifa, shin me ya sa munanan masifu suka sake faruwa a cikin wannan babbar kasa mafi karfi a duniya?

Hakika amsar wannan tambaya, tana daga matakan da ‘yan siyasar kasar suka dauka.

Me ya sa munanan masifu sake faruwa a Amurka?_fororder_2

An lura cewa, ‘yan siyasar kasar su kan mayar da siyasa da moriyar kashin kansu da farko, tun farkon bazuwar annobar COVID-19, ba su dauki matakai a kan lokaci ba, a yayin da jihar Texas ta yi fama da zubar dusar kankara da daukewar wutar lantarki, an ga ‘dan majalisar dattijai na jihar Ted Cruz ya gudu zuwa Mexico domin yawon shakatawa.

Yanzu haka rarrabuwar kawuna tana kawo tarnaki ga daukacin manufofin dake shafar moriyar jama’a a kasar Amurka, kuma an gano ainihin yanayin da al’ummun kasar ke ciki daga tsarin dimokuradiya da ‘yancin kai da hakkin bil Adama salon Amurka. Dalilin da ya sa haka shi ne masu fada a ji a kasar, sun kasa kula da rayuka da tsaro da moriya na al’ummun kasar, amma illar hakan za ta koma kan su, saboda al’ummun kasar za su yi watsi da su.(Jamila)