logo

HAUSA

Jam’iyyar JKS ta Sin na samun yabon masana kan kwarewar shugabanci

2021-02-22 15:22:03 CRI

Masu hikimar magana na cewa, “gani ya kori ji.” Shekaru 40 na baya bayan nan sun kasance tamkar zinariya ga al’ummar Sinawa musamman bisa manyan nasarorin da kasar Sin ta cimma cikin wadannan shekaru ta fannin bunkasuwar tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar al’umma, da ci gaban fasahohin zamani, da kirkire-kirkire, da makamantansu. Wadannan nasarorin sun yi matukar daukar hankalin duniya. Sai dai a bayyane take nasarorin sun ta’allaka ne bisa ga tsarin managarcin shugabanci na mahukuntan kasar karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS mai mulkin kasar. Ko a ’yan kwanakin da suka gabata wani kwararren masanin siyasar kasar Sudan ya bayyana kwarin gwiwa game da kwarewar da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC ke da shi wajen ci gaba da inganta tsarin shugabanci bisa amfani da salon kwarewar da take da shi, ta cimma manyan nasarorin bunkasa tattalin arziki da zaman rayuwar al’umma, kana ta kyautata yin sauye sauye da bude kofarta. Abdul-Khaliq Mahjoub, wani shehun malami ne a fannin siyasa a cibiyar nazarin kimiyyar siyasa dake Khartoum, ya ce shekarar 2021 ta yi daidai da cika shekaru 100 da kafuwar JKS, kuma ta kasance wani muhimmin lokaci bisa lura da irin rawar da jam’iyyar ta taka, ba wai ga kasar Sin kawai ba har ma ga duniya baki daya. Ya ce a cikin shekaru 100 da suka gabata, jam’iyyar CPC ta yi nasarar jagorantar kasar Sin wajen kaiwa matakai iri daban daban na ci gaba da samun makoma mai haske ta hanyar wasu ingantattaun tsare-tsare masu alfanu. Mahjoub ya bayyana kwarewar da jam’iyyar CPC ta nuna a yaki da annobar COVID-19 a matsayin wata hujja dake kara tabbatar da karfin da jam’iyyar ke da shi wajen tinkarar manyan batutuwa. A cewar masanin, tun bayan barkewar annobar, jam’iyyar ta yi ta kokarin zaburar da rassanta dake yankuna daban daban na kasar domin taimakawa shirin dakile annobar da kuma karfafawa Sinawa gwiwa don kawar da annobar COVID-19 daga kasar. Ko shakka babu, JKS ta taka rawar gani ga salon ba da jagoranci wanda ya taimaka wajen kyautata rayuwar al’umma, ba ma Sinawa kawai ba, har ma al’ummar duniya baki daya. (Ahmad Fagam)