logo

HAUSA

Cibiyar kirkire-kirkire ta hadin gwiwar Sin da Afrika za ta samar da himma ga kasashen Afirka wajen raya kansu

2021-02-21 20:56:46 CRI

Cibiyar kirkire-kirkire ta hadin gwiwar Sin da Afrika za ta samar da himma ga kasashen Afirka wajen raya kansu_fororder_微信图片_20210221201045

A ranar Alhamis da ta wuce, an kaddamar da cibiyar kirkire-kirkire ta hadin gwiwar Sin da Afrika a birnin Wuhan, hedkwatar lardin Hubei na kasar Sin, a wani kokari na aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya” da kuma gina kyakkyawar makoma ta bai daya a tsakanin sassan biyu. An ce, lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin ya dade yana aiwatar da hadin gwiwa da kasashen Afirka ta fannoni daban daban, hadin gwiwar da tuni ya samu tarin nasarori ta fuskokin kimiyya da fasaha da masana’antu da al’adu da sauransu, wanda kuma ta aza ingantaccen tushe ga kafa cibiyar a lardin.

A gun bikin bude taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da ya gudana a shekarar 2018 a birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wasu manyan matakai takwas da za a dauka ta fannin hadin gwiwar sassan biyu, ciki har da inganta kwarewar raya kasa, kuma cibiyar kirkire-kirkire ta hadin gwiwar Sin da Afirkar da aka kafa tana daya daga cikin fannoni na matakin inganta kwarewar raya kasa.

Karancin yin kirkire-kirkire na daya daga cikin abubuwan dake yiwa kasashen Afirka tarnaki da dabaibayi wajen raya kansu. A sakamakon rashin ci gaban harkokin kimiyya da fasaha, kasashen Afirka sun dade suna dogara kan fitar da danyun kayayyaki. Sannan kuma sakamakon karancin zuba jari ga harkokin nazarin kimiyya, ya sa masanan nazarin kimiyya da yawa sun fita zuwa ketare. Amma a cikin ’yan shekarun baya, shugabannin kasashen Afirka da al’ummunsu sun fara fahimtar muhimmancin bunkasa harkokin kimiyya da fasaha, abin da ya sa suka kara zuba jari ga aikin kirkire-kirkiren fasahohi, don fatan ganin ci gaban kimiyya da fasaha ya sa kaimin bunkasuwar tattalin arziki da zaman al’umma. A sa’i daya kuma, kasar Sin na aiwatar da manufar raya kasa bisa yin kirkire-kirkire, tare da cimma gagaruman nasarori. Musamman ma a yayin da kasar ta aiwatar da shirinta na raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 13, kasar ta cimma nasarorin a zo a gani ta fannin nazarin kimiyya da fasaha, har ma ta shiga sahun gaba a duniya ta fannin kirkire-kirkire. Wani rahoton da kungiyar kare hakkin mallakar ilmi da fasaha ta duniya ta fitar dangane da matsayin kirkire-kirkiren kasashen duniya a shekarar 2020 ya yi nuni da cewa, daga cikin kasashe 131, kasar Sin ta kai matsayi na 14, wadda ta kasance kasa mai matsakaicin kudin shiga daya tilo da ta shiga jerin kasashe 30 da ke kan gaba.

An ce, cibiyar kirkire-kirkire da hadin gwiwa ta Sin da Afrika za ta samar da dandamali biyu ta kafar intanet da wanda ba na intanet ba, domin inganta kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da hadin gwiwa, da zuba jari ta fuskar samar da kayayyaki da musayar fasaha tsakanin matasan bangarorin biyu.

Sinawa kan ce, “Da samar da kifi ga wani, gwamma a koya masa fasahar kamun kifi.” Kwarewar raya kasa ya kasance tushen bunkasa tattalin arziki da zaman al’umma, don haka kuma ya shafi fannoni daban daban na hadin gwiwar Sin da Afirka. Babu shakka, cibiyar kirkire-kirkire da hadin gwiwa ta Sin da Afrika da aka kafa za ta taimaka ga kara inganta hadin gwiwar sassan biyu, tare da samar da himma ga bunkasuwar kasashen Afirka, haka kuma za ta taimaka wajen gina kyakkyawar makoma ta bai daya a tsakaninsu. (Lubabatu Lei)