logo

HAUSA

Sadaukarwar jarumai ba za ta taba gushewa a zukatanmu ba

2021-02-20 19:52:40 CRI

Sadaukarwar jarumai ba za ta taba gaushewa a zukatanmu ba_fororder_1

Babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice ya wallafa wani shiri mai sosa rai sosai jiya Jumma’a, inda ya nuna yadda sojojin kasar suka sadaukar da rayukansu don kare cikakken ‘yancin kasa. Shirin nan yana bazuwa a shafin sada zumunta, har ma ya janyo matukar bacin-rai da takaici a tsakanin al’ummar kasar Sin, musamman a wannan lokacin da al’ummun kasar suke ci gaba da murnar bikin bazara, wato bikin shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya.

Shirin ya shaida wani rikicin da ya barke a watan Yunin shekara ta 2020, inda a wani kwarin kogi mai suna Galwan dake yankin iyakokin Sin da Indiya, wasu sojojin Indiya suka tsallake iyakar har suka kafa tantuna a bangaren kasar Sin. Kwamandan rajamanti na rundunar sojojin dake tsaron baki iyakar kasar Sin, Qi Fabao da sauran wasu sojoji hudu sun je yi musu magana ba tare da daukar makamai ba, amma a wajen yin sulhu, sojojin Indiya suka yi wa sojojin kasar Sin harin kwanton-bauna ba zato ba tsammani, abun da ya yi ajalin sojojin kasar Sin hudu, tare da jikkata Qi Fabao sosai.

Sojojin kasar Sin ba yadda za su yi sai dai kawai su maida martani da fatattakar sojojin Indiya, inda bangaren Indiya ya bar wasu sojojinsa a fagen fama. Lamarin da ya sa kasar Sin ta ba su jinya da kulawa, tare kuma da maida su gami da makamansu gida.

Amma abun takaici shi ne, rahotannin da kafofin watsa labaran Indiya da na wasu kasashen yammacin duniya suka ruwaito sun ce, wai sojojin Indiya sun kashe sojojn kasar Sin sama da 10, abun da ya sa suka samu “nasara” a fagen yaki. Har ma bangaren Indiya ya karramawa wasu sojoji da lambar yabo da ake kira “jaruman Galwan”. Saboda haka, bayan watanni 8 na aukuwar lamarin, kasar Sin ta wallafa labari game da wannan rikici, don karyata jita-jita da labaran bogi, duk da cewa har kullum tana da sahihiyar niyyar kiyaye dangantakarta da Indiya gami da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin iyakokin kasashen biyu.

Sadaukarwar jarumai ba za ta taba gaushewa a zukatanmu ba_fororder_2

A halin yanzu Sinawa suna ci gaba da murnar shiga sabuwar shekara bisa kalandarsu ta gargajiya, amma kar mu manta, su sojojin kasar suna himmatuwa wajen tabbatar mana da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da kuma kiyaye cikakken ‘yancin kasa da mutuncinta. A wannan rikicin, sojojin kasar Sin hudu sun sadaukar da ransu, ciki har da Chen Hongjun, da Chen Xiangrong, da Xiao Siyuan, da kuma Wang Chaoran, wadanda ba za mu manta da sunayensu ba har adaba. Su ne ‘ya’yan mahaifansu, su ne mazajen matansu, su ne iyayen ‘ya’yansu, su ne suka sadaukar da rayukansu domin ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali, wadanda kuma suka shaidawa duk duniya kwazo da karfin da sojojin kasar Sin suke da su.

Jamhuriyar jama'ar kasar Sin hamshakiyar kasa ce a duniya, amma ba ta taba kutsa kai cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe ba, kana ba ta taba kai hari kan sauran kasashe ba. Amma ba ta tsoron duk wata barazana ko kuma wutar rikicin da za a hura don takalarta, kuma ba za ta taba ba.  Duk wani mutum ko wata kasa da ta tada rikici ko kawo barazana ga kasar Sin, komai nisanta, Sin za ta mai da martani yadda ya kamata! (Murtala Zhang)