logo

HAUSA

Kasar Sin ta zama aminiyar cinikayya mafi girma ta EU

2021-02-19 21:43:00 CRI

Kasar Sin ta zama aminiyar cinikayya mafi girma ta EU_fororder_1

Hukumar kididdiga ta kungiyar tarayyar Turai wato EU, ta bullo da alkaluman kasuwanci a kwanan nan, inda a cikinsa aka nuna cewa, a shekara ta 2020, a karo na farko kasar Sin ta maye gurbin Amurka, inda ta zama aminiyar cinikayya mafi girma ta EU.

A cikin manyan aminan cinikayya goma na EU, kasar Sin ita kadai ce ta samu karuwar cinikin shige da fice dukka. A shekara ta 2020, darajar hajojin da EU ta shigo da su daga kasar Sin, ta kai kudin EURO biliyan 383.5, adadin da ya karu da kaso 5.6 bisa dari. Kuma darajar hajojin da EU ta fitar da su zuwa kasar Sin ta kai kudin EURO biliyan 202.5, adadin da shi ma ya karu da kaso 2.2 bisa dari.

Dalilin da ya sa kasar Sin ta zama aminiyar cinikayya mafi girma ta EU shi ne, EUn tana matukar bukatar kayayyakin yaki da annobar COVID-19, da sauran wasu abubuwan lantarki, al’amarin da ya taimakawa kasar Sin ta fitar da wadannan hajoji zuwa kasashen Turai.

Kasar Sin ta zama aminiyar cinikayya mafi girma ta EU_fororder_2

A dayan bangaren kuma, kasar Sin ta yi nasarar dakile yaduwar cutar, da farfado da ayyukan kasar da harkokin sayayya cikin sauri, abun da ya samar da babbar kasuwa ga motoci kirar kasashen Turai.

Babu shakka, hakan na da alaka sosai da matukar kokarin da bangarorin biyu wato Sin da Turai suka yi tare, gami da tushe mai inganci dake tattare da kasuwancinsu.

Bunkasar kasuwancin Sin da Turai ya shaida cewa, a yayin da ake kara samun dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya, ya dace kasa da kasa su nunawa juna hakuri da neman samun moriyar juna.

A matsayinsu na wasu manyan kasuwanni biyu a duk fadin duniya, fadada hadin-gwiwa tsakanin Sin da Turai, zai amfane su sosai ga farfadowar tattalin arzikin duniya, da kara saukaka matakan kasuwanci da zuba jari, tare kuma da bayar da babbar gudummawa ga raya tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa ga kowa da kowa.(Murtala Zhang)