logo

HAUSA

Ngozi Okonjo-Iweala : “Akwai bukatar mu yi kokari tare don cimma nasarar muhimman ayyuka dake gabanmu.”

2021-02-19 19:17:19 CRI

Bayan watanni takwas ana aikin tantancewa, tsohuwar Ministar Kudin Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala ta zama darakta janar ta bakwai ta kungiyar WTO. Ga sabuwar shugabar hukumar, yadda za a tabbatar da gudanarwar cinikayyar duniya yadda ya kamata a halin da ake ciki na yakar annobar COVID-19, da inganta farfadowar tattalin arzikin duniya, da cinikayya cikin sauri, zai kasance babban kalubale a gaban ta.

Ngozi Okonjo-Iweala : “Akwai bukatar mu yi kokari tare don cimma nasarar muhimman ayyuka dake gabanmu.”_fororder_rBABCmAqhVuAOBVqAAAAAAAAAAA036.1200x800.750x500

Bisa wani sabon rahoto da kungiyar WTO ta fitar a baya game da bayanan cinikayya na duniya, da kuma hangen nesa a fannin, ya yi hasashen cewa, yawan cinikayyar kayayyaki a duniya zai ragu da kashi 9.2% a shekarar 2020, sakamakon yaduwar annobar ta COVID-19.

A sa’i guda kuma, har yanzu akwai rashin tabbas kan makomar farfadowar tattalin arzikin duniya, sakamakon yaduwar annobar da matakan rigakafi da kasashe daban daban za su dauka da dai sauransu.

A cikin sanarwar da ta bayar, Okonjo-Iweala ta sha alwashin cewa, za ta ba da tabbaci wajen ganin kungiyar WTO ta ba da gudummawa ga tsarin cinikayya na bangarori daban-daban gwargwadon karfinta, da tinkarar kalubalen da annobar ke kawowa, ta fuskokin tattalin arzikin duniya, da kiwon lafiyar al’umma.

A yayin da ake yaki da annobar, matakan takaita kasuwanci da wasu kasashe suka dauka kan magunguna da bukatun yau da kullum, sun kawo cikas ga hadin kan duniya wajen yaki da cutar. Dangane da wannan, Okonjo-Iweala, ta bayyana fatan ta na hada kai da kasashe mambobin kungiyar, wajen tsarawa da aiwatar da matakan da suka dace, don sanya tattalin arzikin duniya ya gudana yadda ya kamata.

Ngozi Okonjo-Iweala : “Akwai bukatar mu yi kokari tare don cimma nasarar muhimman ayyuka dake gabanmu.”_fororder_src=http___5b0988e595225.cdn.sohucs.com_images_20180702_489e7a42e03f42c4af8c1428f83cc60e.jpeg&refer=http___5b0988e595225.cdn.sohucs

Kafin haka, a yayin da take zantawa da kamfanin dillacin labarai na Xinhua, Okonjo Iweala ta ce, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen tinkarar wannan matsala ta duniya. Ba kawai kasar Sin ta takaita wajen fitar da magunguna da na’urorin aikin jinya zuwa kasashen waje ba ne, har ma tana taimakawa kasashe masu tasowa wadanda ba za su iya samun wadannan kayayyakin ba. A lokaci guda, saurin farfado da tattalin arzikin da kasar Sin ke samu, ya ba da gudummawa matuka ga duniya baki daya.

Wani jami’in sashen kula da harkokin WTO na Ma’aikatar Kasuwancin Kasar Sin, ya taya Okonjo-Iweala murnar zama sabuwar Darakta Janar na WTO, inda ya kuma ce, kasarsa na cike da imanin kan ta, a matsayin darakta-janar na WTO. Kana kasar Sin za ta nuna goyon baya ga tsarin cinikayya na bangarori da dama, da shiga a dama da ita a ayyukan yin kwaskwarima kan kungiyar, da kuma nuna goyon baya ga darakta janar din a aikinta.

Ko da yake wannan mace mai karfin gaske tana fuskantar kalubale wajen aikinta, amma sakamakon kasancewarta a matsayin shugabar kwamitin kungiyar (GAVI) mai rajin samar da alluran rigakafi ga duniya baki daya, wadda ta taba zama kuma manzon musamman a shawarar hadin kan duniya ta “the ACT-Accelerator” a karkashin shugabancin Hukumar Lafiya ta Duniya, dukkansu za su taimake ta wajen karbar jagorancin kungiyar WTO a wannan yanayin da ake ciki na tinkarar annobar.

Ita ma kanta, tana cike da kwarin gwiwa kan wannan nadin, kamar yadda ta fada wa magoya baya ta a shafin sada zumunta: Tana mai cewa "Akwai bukatar mu yi kokari tare, domin cimma nasarar muhimman ayyuka dake gabanmu.” (Bilkisu Xin)