logo

HAUSA

WHO: Afirka na fuskantar kalubale na COVID-19 da Ebola a lokaci guda

2021-02-19 11:55:57 CRI

WHO: Afirka na fuskantar kalubale na COVID-19 da Ebola a lokaci guda_fororder_20210219-WHO-bayani-Bello

Ofishin kula da harkokin Afirka na hukumar lafiya ta duniya WHO, ya bayyana a jiya Alhamis cewa, nahiyar Afirka na fuskantar kalubalen COVID-19 da Ebola a lokaci guda. A cewar ofishin, sai kasashen nahiyar sun hada gwiwa da juna don tinkarar kalubalen yadda ake bukata.

Darektar ofishin kula da nahiyar Afirka na hukumar lafiya ta duniya WHO, Matshidiso Moeti, ta bayyana a wajen wani taron manema labaru cewa, a makon da ya gabata, an samu karin wasu mutane 77000 da suka kamu da cutar COVID-19 a nahiyar Afirka. Kana zuwa yanzu an samu wasu mutane fiye da miliyan 3 da dubu 700 da suka taba kamuwa da cutar a nahiyar. Cikinsu wasu fiye da dubu 99 sun rasa rayuka. Madam Moeti ta ce,

“Cikin watanni 2 da suka wuce, an samu sararawar yanayin bazuwar cutar COVID-19 a wasu kasashen da suka yi matukar jin radadin cutar a baya, wadanda suka hada da Afirka ta Kudu, da Najeriya, da Masar, gami da Tunisia. Amma ana ci gaba da samun karuwar masu kamuwa da cutar sosai a kasashen da suka hada da Zambia, da Togo, da Sudan ta Kudu, da sauransu.”

A cewar Madam Moeti, hukumar WHO ta riga ta sanya allurar rigakafi na Oxford da AstraZeneca cikin jerin magungunan gaggawa, lamarin da zai taimakawa kasashen Afirka samun rigakafi, da fara gudanar da aikin yi wa al’umma allurar.

Sai dai yanzu ana samun bazuwar sabon nau’in kwayar cutar COVID-19, wadda ta sha bamban da ta baya, a nahiyar Afirka. Kana a cikin kasashen da aka gano sabbin kwayoyin cutar COVID-19, annobar ta fi saurin yaduwa, idan an kwatanta da yanayin yaduwar cutar a baya. Zuwa yanzu, kwayar cutar da ta sauya tsarinta, wadda aka fara gano ta a kasar Afirka ta Kudu, ta riga ta yadu zuwa wasu kasashe 8 dake nahiyar Afirka, yayin da sabuwar kwayar cutar COVID-19 da aka gano ta a kasar Birtaniya, ta yadu zuwa wasu kasashe 6 dake nahiyar.

Madam Moeti ta kara da cewa, a ranar 17 ga wata, ministocin lafiya na kasashe daban daban dake nahiyar Afirka, sun gudanar da wani taro, don tabbatar da tsarin da ake bi wajen yi wa jama’ar kasashensu allurar rigakafi. A cewarta,

“Jami’an da hukumarmu ta tura kasashe daban daban na hadin gwiwa da gwamnatocinsu, don gudanar da bincike kan yanayin da ake ciki, ta yadda za a iya yin allurar rigakafin tun da wuri. Zuwa yanzu ana samun sauye-sauyen yanayin kwayoyin cutar, don haka ya kamata mu san wadanne kwayoyin cuta ne ke yaduwa, abun da zai taimakawa daukar nagargattun matakai don tinkarar kalubalen.”

A kwanakin nan, an samu barkewar annobar cutar Ebola a kasashen Guinea da Congo Kinshasa, daga baya hukumar WHO ta tunasar da wasu kasashe 6 makwabtan kasashen 2 da su fara zama kan baka, kasashen da suka hada da Saliyo, da Laberiya, da Senegal, da Guinea Bissau, da Mali, da kuma Kodibwa. A cewar Madam Moeti, a wannan karon, Guinea da Congo Kinshasa sun dauki matakan dakile cutar Ebola cikin sauri, bisa fasahohin da aka samu a baya. Don haka ba zai yiwu a samu bazuwar cutar mai tsanani, kamar yadda aka taba gamuwa da ita a baya ba. Ban da wannan kuma, Madam Moeti ta ce, za a yi jigilar allurar rigakafin cutar Ebola fiye da dubu 11 daga Geneva na kasar Switzerland zuwa Guinea. A cewar wani jami’i na kasar Guinea, ana sa ran ganin isar allurar rigakafin a kasarsa a ranar 21 ga wata, kana za a fara yi wa jama’ar kasar allura a ranar 22 ga watan da muke ciki.

A nata bangare, Madam Moeti ta kara da cewa, za a tinkari cututtukan COVID-19 da Ebola a lokaci guda, ta hanyar hadin gwiwar hukumomin lafiya na kasashen Afirka. Ta ce,

“Kasashen dake yammacin Afirka sun riga sun kafa cibiyoyin daukar matakai cikin gaggawa, da kungiyoyin likitoci, wadanda ke da kwarewa a fannin allurar rigakafi. Ta wadannan hanyoyi, za a hada ayyukan tinkarar COVID-19 da Ebola waje guda.” (Bello Wang)

Bello