logo

HAUSA

Sin na ci gaba da ba da gudummawa a yakin da duniya ke yi da COVID-19

2021-02-18 18:34:21 CRI

Sin na ci gaba da ba da gudummawa a yakin da duniya ke yi da COVID-19_fororder_微信图片_20210218181212

A ranar Laraba, dan majalissar gudanar kasar Sin kuma ministan wajen kasar Wang Yi, ya halarci zaman tattaunawa na kwamitin tsaron MDD ta kafar bidiyo, taron da ya maida hankali ga batun yaki da cutar numfashi ta COVID-19, kuma a yayin taron a nata bangare, Sin ta jaddada kudurin ci giba da maida rigakafin cutar da ake sarrafa a kasar na dukkanin al’ummar duniya.

Wani abu da ya ja hankalin masharhanta game da wannan zama shi ne, shawarwarin da ministan harkokin wajen na Sin ya gabatar, game da matakan cimma nasarar yaki da wannan annoba.

Jami’in na Sin ya ce, kamata ya yi sassan kasa da kasa su rungumi manufar sanya al’umma gaban komai, da karfafa hadin gwiwa wajen yaki da COVID-19. Har ila yau ya ce kamata yayi kwamitin na tsaro, ya samar da yanayi mai kyau na yaki da annobar. Kana a warware matsalar rashin daidaito a fannin raba rigakafin, da samar da isassun rigakafin ga kasashe masu tasowa. Har ila yau akwai bukatar karfafa tsare tsare da gudummawar MDD a wannan fanni.

Sin na ci gaba da ba da gudummawa a yakin da duniya ke yi da COVID-19_fororder_微信图片_20210218181205

Ko shakka ba bu, wadannan shawarwari na dada haskaka matsayin kasar Sin, na nacewa daukar managartan matakan tabbatar da duniya ta amfana daga rigakafin COVID-19 a kan lokaci, ba kuma tare da sanya siyasa, ko takarar kasuwa cikin batun rigakafin ba. Shawarwarin sun kuma yi daidai da aniyar hukumar lafiya ta duniya WHO, wadda karkashin shirye shiryen ta, ta tsara wani shirin samar da rigakafin COVID-19 mai lakabin COVAX, da nufin samar da rigakafin cutar ga kasashe marasa wadata, ciki har da kasashe masu tasowa.

Da ma dai tuni kasar Sin ta sha alwashin samar da rigakafin COVID-19, wanda dukkanin sassa duniya za su iya samu cikin rahusa, a matsayin gudummawar ta ga yakin da duniya ke yi da wannan annoba.

Kamar dai yadda Bahaushe kan ce “Hannu daya baya daukar jinka”, la’akari da wadannan shawarwari da minista Wang ya gabatar, ana iya kara fahimtar himmar kasar Sin, ta ci gaba da aiki tare da sauran sassan masu ruwa da tsaki, wajen tabbatar da nasarar rigakafin da aka fara, da kuma wanzuwar matakan kandagarkin annobar.

Fatan dai shi ne, su ma sauran kasashe masu wadata, da wadanda suke sarrafa rigakafin wannan annoba a cikin gida, za su yi koyi da Sin, wajen maida rigakafin da suke samarwa hajar da dukkanin bil Adama zai iya cin gajiyar ta. Su shiga shirin COVAX na WHO gadangadan, don ba da gudummawar rigakafin ga sauran kasashe masu tasowa, ta yadda alfanun ta zai iya karade dukkanin sassan duniya, har a kai ga kawo karshen yaduwar wannan annoba ta COVID-19 cikin sauri. (Mai fassara: Saminu)