logo

HAUSA

Li Gang: Ina Fatan Karin Mutane za su So Wasan Kankara

2021-02-18 12:33:29 CRI

Li Gang: Ina Fatan Karin Mutane za su So Wasan Kankara_fororder_微信图片_20210217212321

Li Gang, dan shekaru sama da 30, yana aikin horas da ‘yan wasan kankara cikin sauri, a wata kungiyar koyon fasahohin wasan kankara cikin sauri ta birnin Beijing.

Da farko dai, yana koyar da yara wasan gudu kan kasa da taya kan takalma tun daga shekarar 2010. Ya kware a wasan tun yana karatu a jami’ar wasannin motsa jiki ta birnin Beijing. Kasancewar yana son wannan wasa sosai, ya koye shi a yayin da yake jami’a, kana ya yi amfani da koyar da yara wannan wasa a cikin kungiyar koyar da yara wasan don samun kudi, da ci gaba da yin karatu da rayuwa a birnin Beijing.

A lokacin, ya gano cewa, yara da dama suna son wannan wasa. Saidai bayan da ya gama karatu a jami’a, ya yi amfani da kudin da ya ajiye, ya kafa wata kungiyarsa ta koyar da fasahohin wasan. A lokacin yanayin bazara da zafi da kaka, ya na horas da yara wasan gudu kan kasa da taya kan takalma, kuma a lokacin sanyi wato hunturu, yana koya wa yara wasan kankara cikin sauri. Amma a ranar Asabar da Lahadi, yana yin kos a cikin dakin wasa, saidai dukkan wasanni biyu yana iya koyawa ba tare da yin la’akari da yanayi ba.

Da farko dai, shi da sauran abokansa biyu sun kafa kungiyar koyar da wasan gudu kan kasa da taya kan takalmai da wasan kankara cikin sauri tare, sunan kungiyar da farko shi ne “Xuanku”. Bayan shekaru biyu ko uku, abokansa sun janye daga kungiyar, saidai Li Gang shi da kansa ya ci gaba da aiwatar da harkokin kungiyar, da kuma canja sunan kungiyar da sunan “Kuai Xing Zhe”, ma’anarsa ita ce yin wasa cikin sauri. Ya yi kokarin raya kungiyar da kansa har na tsawon shekaru biyar ko shida, ya zuwa yanzu yawan daliban da suke koyon fasahohin wasa a cikin kungiyarsa ya kai fiye da 400. A shekara daya da ta gabata, ya kara shigar da wasu malamai uku don bada horaswa ga dalibansu tare. Ya ce, ya zuwa yanzu tawagarsa ta kunshi mutane shida, wadanda aka raba su aiki iri daban daban don aiwatar da harkokin kungiyar tare. Li Gang ya ce,“An rabawa mu shida ayyuka daban daban, kamar su bada horaswa, da shirya jadawalin kos, da sauransu. Kuma mun raba ajin yara a matsayin ajin na farko, da ajin na matsakaita, da kuma ajin kwararru. A cikin ajin kwararru, muna da tawaga ta farko da kuma tawaga ta biyu. Yara dake cikin tawaga ta farko za su halarci gasar wasan ta kasar ko ta birane. Akwai wasu da suka zamo zakaru, ko matsayi na biyu a gasanni na birane, lambar yabo mafi kyau ita ce matsayi na biyu da wani ya samu a gasar wasan ta yara ta kasar Sin.”

Li Gang shi ba ya taba samun lambobin yabo a wasan gudu wasan gudu kan kasa da taya kan takalmai ko wasan kankara cikin sauri ba, domin ya koyi fasahohin bada ilmi da horaswa a jami’a, don haka ya zama malamin bada ilmi da bada horaswa bayan da ya gama karatunsa a jami’a.

Ya ce, bayan shekaru biyar yana bada horo ga wasan gudu kan kasa da taya kan takalmai, ya fara koyon fasahohin wasan kankara cikin sauri, domin wadannan wasanni biyu suna da nasaba da juna, wato an yi wasan gudu a kan kasa ko a kan kankara. Ya ce, domin a lokacin hunturu a birnin Beijing, ana samun kankara a birnin, saidai an fara koyar da yara da wasan gudun kankara.

Li Gang: Ina Fatan Karin Mutane za su So Wasan Kankara_fororder_微信图片_20210217212334

Game da dalilin da yasa ya canja koyar da wasan gudu kan kasa zuwa wasan kankara, Li Gang ya bayyana cewa,“Tun daga shekarar 2008, kasar Sin ta yi kira ga canja wasan gudu kan kasa da taya kan takalmai zuwa wasan gudu kan kankara, saidai mun fara yin kokarin gyara kos dinmu, mun kara shigar da kos na koyar da wasan kankara cikin sauri, don haka mun bude kos dinmu a cikin dakin wasa don koyar da wasan kankara cikin sauki.”

Li Gang ya kara da cewa, koda yake ba ya samu kudi da dama daga aikin koyar da yara wasan kankara ba, amma yana son yara za su iya yin wasan gudu kan kasa da kan kankara baki daya.

Li Gang ya ce, ya yi sauki ne da iya yin wasan, amma idan ana son zama gwani a wasan, saidai ya kamata a kara yin kokarin koyon fasahohin wasan. Ya ce, alal misali, idan wani yaro mai shekaru 6 da haihuwa yana son halartar gasar wasan ta birnin, ya kamata ya yi kokarin koyon wasan fiye da shekara daya, kwatankwacin shiga kos sau fiye da dari daya. Kwalliya tana biyan kudin sabulu, ya ce idan yara sun yi kokari da kuma kiyaye yin shi ba tsayawa ba, saidai za su cimma samun sakamako mai kyau. Li Gang ya kan samar da dama ga yara da su iya halarci gasanni da dama, don inganta fasahohinsu. Ya ce, yana fatan dalibansa ko akwai wani ya iya cimma zakara a gasar wasan ta kasar Sin a nan gaba.

Game da rawar da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu da za a gudanar a birnin Beijing a shekarar 2022 ke takawa, Li Gang ya ce, an kara sa kaimi ga mutane da su shiga wasan kankara. Ya ce,“An kara sa kaimi ga mutane da su shiga wasan kankara. Tun daga shekarar bara, an kara samun mutane musamman yara dake fara shiga wasan kankara da yin kos a kungiyarmu. A bana, tun ma lokacin hunturu bai zo ba, sai iyalan yara da dama sun tambaye mu ko yaushe ake iya fara yin kos na wasan kankara a waje. A ganina, mutane ke kara son wasan kankara a lokacin da kusan kaddamar da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing.”

Li Gang yana da wata yarinya, ya ce ‘yarsa ta fara koyon wasan gudu kan kasa da da taya kan takalmai tun daga yawan shekarunta ba su wuce biyu kacal ba, yanzu ‘yarsa tana sha’awar wasan sosai. Yanzu ta cika shekaru 3 da haihuwa, saida ta shiga ajin farko na kungiyar Kuai Xing Zhe.

Game da matsalolin da yake fuskanta, Li Gang ya ce, filayen wasan da suke yin kos da kuma neman malaman koyar da wasan su ne manyan matsalolin da ke gabansu. Ya ce, abu ne mai wuya a samu filin wasa mai dacewa da ake iya yin kos a birnin Beijing, kana malaman da suke bada kos ba su kiyaye yin aiki a kungiya a dogon lokaci ba, wasu sun janye daga kungiyar da yin aiki na daban, wasu sun kafa kungiyoyinsu. Don haka, Li Gang ya yi hadin gwiwa tare da sauran kungiyoyin koyar da fasahohin wasan gudu kan kasa da kan kankara, da more malamai da filayen wasa, da daidaita ajin koyarwa don warware matsalolin da suke fuskanta.

Wata mahaifiyar yariniya mai koyon wasan a kungiyar Li Gang ta ce, ‘yarta tana son wasan kana tana son koyon fasahohi tare da malam Li. Ta ce,“Tana sha’awar wasan kankara sosai. Kana bayan da ta fara koyon fasahohin wasan kankara, a ganina ta kara samun jaruntaka. Domin akwai wuya a iya tafiya a kan kankara, sai ta iya magance tsoronta, da yin gudu a kan kankara, kana ta iya daidaita matsalolinta a yayin da take fuskantar kalubale a nan gaba. Kana kuma ta kan more lamarinta yayin da take koyon wasan kankara tare da abokan karatunta.”

Wata mahaifiyar yariniya mai koyon wasan ta daban ta ce, wasan kankara zai inganta karfin jikin yara. Ta ce,“A ganina, ya kamata kowa ya yi motsa jiki a yau da kullum, musamman yara. Wasan kankara hanya mai kyau ga yara, da kiyaye yin motsa jiki da kiyaye lafiyar jikinsu.”

Li Gang: Ina Fatan Karin Mutane za su So Wasan Kankara_fororder_微信图片_20210217212340

Meng Siyou ta fara koyon wasan kankara tun tana da shekaru hudu kacal, ta ce yanzu tana sha’awar wasan sosai. Ta ce,“Da farko, ban iya yin tafiya ko kadan a kan kankara ba, amma bayan da na koya wasan kankara, na iya yin tafiya har ma da iya yin gudu cikin sauri ba tare da dogaro saura ba, na ji dadi sosai. Yanzu ina sha’awan wasan sosai.”

Game da burinsa, Li Gang ya bayyana cewa, da farko dai yana son yada wasan kankara a tsakanin jama’a, da kara sa mutane su san wannan wasa, amma yanzu yana son karin mutane ke son wasan kankara da shiga wasan, ko yara ko balagai, da maida wasan a matsayin kashi daya daga cikin rayuwarsu. Kana yana fatan yaran da ya koyar da su za su iya shiga kungiyar wasan ta birnin Beijing ko kuma kungiyar wasan ta kasar Sin, da kuma za a kara gina filayen wasan kankara da dakunan wasan a dukkan kasar Sin da kara samar da dama ga Sinawa ke iya shiga wasan cikin sauki.(Zainab Zhang)