logo

HAUSA

Yawan Kudin Da Sinawa Suka Kashe A Yayin Hutun Bikin Bazara Ya Shaida Bunkasar Tattalin Arzikin Kasar

2021-02-18 21:54:11 CRI

Yawan Kudin Da Sinawa Suka Kashe A Yayin Hutun Bikin Bazara Ya Shaida Bunkasar Tattalin Arzikin Kasar_fororder_A

A yayin hutun bikin bazara na kasar Sin, wato bikin murnar shiga sabuwar shekara ta saniya bisa kalandar gargajiyar kasar, Sinawa sun kashe makuden kudade a fannin cin abinci da sayen abubuwa da ya zarce Yuan biliyan 800.

Yawan Kudin Da Sinawa Suka Kashe A Yayin Hutun Bikin Bazara Ya Shaida Bunkasar Tattalin Arzikin Kasar_fororder_B

Alkaluman kididdigar da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, a yayin hutun bikin bazara na kwanaki 7, yawan kudaden da Sinawa suka kashe a bangarorin sayen abubuwa da cin abinci ya kai kimanin Yuan biliyan 821, adadin da ya karu da kaso 28.7 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. A farkon shekarar da muke ciki bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, harkokin sayayya sun bunkasa kamar haka, abun da zai samar da babban kuzari ga ci gaban tattalin arzikin kasar a sabuwar shekara.

Yawan Kudin Da Sinawa Suka Kashe A Yayin Hutun Bikin Bazara Ya Shaida Bunkasar Tattalin Arzikin Kasar_fororder_C

Sinawa da yawansu ya kai biliyan 1.4 sun zama babban karfi wajen habaka tattalin arzikin kasarsu. A shekarar da ta gabata, duk da cewa annobar COVID-19 ta haifar da babban kalubale, amma yawan kudaden da Sinawa suka kashe wajen sayen abubuwa ya dauki kaso 54.3 bisa dari na yawan GDPn kasar, wanda ya kai matsayin koli a ‘yan shekarun da suka wuce. Kuma rahoton da kamfanin samar da hidimomin kudi na Morgan Stanley ya fitar, an yi hasashen cewa, nan da shekaru 10 masu zuwa, matsakaicin karuwar yawan kudaden da Sinawa za su kashe wajen sayen abubuwa a kowace shekara, zai kai kaso 7.9 bisa dari, wanda ke zama kan gaba a fadin duniya baki daya.

A matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, bunkasar harkokin sayayya na kasar Sin wani albishiri ne ga tattalin arzikin duniya. Sinawa suna kara maida hankali kan ingancin kayayyaki, kuma suna kara bukatar sayen abubuwa kirar kasashen waje. A don haka, muddin ‘yan kasuwar kasashen duniya suka kara fahimtar kasuwannin kasar Sin, da sanin abubuwan da Sinawa suke so, za su gano cewa kasuwar Sin kasuwa ce ta ainihi ta kasa da kasa, wadda ke cike da karfi da kuzari da damammaki masu tarin yawa. (Murtala Zhang)