logo

HAUSA

Nadin Ngozi Okonjo Iweala Matsayin Shugabar WTO, Sanya Kwarya Ne A Gurbinta

2021-02-16 14:46:35 CRI

Nadin Ngozi Okonjo Iweala Matsayin Shugabar WTO, Sanya Kwarya Ne A Gurbinta_fororder_0216-1

Bayan shafe watanni shida ba tare da shugaba ba, a jiya Litinin, kungiyar kula da cinikayya ta duniya WTO, ta samu sabon shugaba, inda aka nada Ngozi Okonjo Iweala a matsayin sabuwar shugabar hukumar.

Ngozi Okonjo-Iweala, mai shekaru 66, ‘yar asalin Nijeriya, ta kasance mace ta farko kuma ‘yar Afrika ta farko da za ta shugabanci kungiyar mai tarihin shekaru 26 da kafuwa.

Sabuwar Shugabar kungiyar WTO, kwararriya ce kan harkokin kudi, lamarin da ya kai ta ga shefe shekaru 25 tana aiki a Bankin Duniya, har ta kai matsayi na biyu mafi girma a bankin. Kana ta rike ministar kudin Nijeriya har sau biyu, inda ta zama mace ta farko da ta rike mukamin.

Hakika nadin nata a matsayin shugabar WTO, tamkar dora kwarya ne a gurbinta, bisa la’akari da halin da hukumar ke ciki da kuma sanin da aka yi mata na kwararriya kuma jajirtacciya kan aikinta. An ga irin wannan namijin kokari da tsayawa da tsayawa tsayin daka a lokacin da ta yi aiki a Nijeriya, inda ta sha gwagwarmaya da aiwatar da wasu ayyuka kamar na cimma yarjejeniyar kawar da wani dadadden bashi da ake bin kasar da kaddamar da wani tsari na fitar da dubban ma'aikata da 'yan fansho na bogi daga tsarin aikin gwamnatin kasar, da kuma yaki cin hanci da rashawa.

Ngozi Okonjo Iweala, ta zo a lokacin da hukumar WTO ke matukar bukatar garambawul, bisa la’akari da matsalolin da take fuskanta kamar na fafutukar cimma yarjeniyoyi da barazana da suka daga Amurka, da kuma uwa uba bullar cutar COVID-19. Don haka akwai jan aiki a gabanta. Sai dai nagartarta da kwarewa, abu ne mai bayar da kwarin gwiwa game da kasancewarta kan mukamin.

Ana da yakinin cewa, za ta kawo wasu sabbin sauye-sauye masu alfanu ga kungiyar WTO da ba a taba gani ba a baya, da tabbatar da daidaito tsakanin mambobin kungiyar, da kuma dawo da karfinta na fada a aji a fannin cinikayya, inganta cinikayya tsakanin kasashe bisa daidaito da adalci, wadanda abubuwa ne da mambobin kuniyar kamar Sin suka dade suna nema.

Duk da cewa a yanzu ba Nijeriya kadai take wakilta ba, nadin na ta zai kara daukaka matsayin kasarta a idon duniya. Sannan zai ba kasashe masu tasowa kwarin gwiwar cin gajiyar harkokin cinikayya da sauran tsare-tsaren hukumar, haka kuma, za a rika jin amonsu a harkokin cinikayya na duniya.

Bugu da kari, wannan nadin tamkar zaburarwa ce ga mata a fadin duniya, domin zai ba su kwarin gwiwar kara jajircewa, sanin cewa, ilimi da kwarewarsu zai ba su damar kai wa wani matsayi da takwarorinsu maza ne kadai ke kaiwa a baya. Hakika wannan ya nuna cewa, an fara samun ci gaba a fannin tabbatar da daidaiton jinsi da kawar da wariya, duk da cewa, har yanzu da sauran rina a kaba, wannan wata alama ce dake cewa, za a kai inda ake muradi ta fuskar damawa da mata a muhimman makuman da suka shafi duniya baki daya.(Fa'iza Mustapha)