logo

HAUSA

Bikin bazara na musamman ya nuna ingancin tsarin tafiyar da harkokin kasar Sin

2021-02-14 16:23:21 CRI

Bikin bazara na musamman ya nuna ingancin tsarin tafiyar da harkokin kasar Sin_fororder_1

Bikin bazara wato bikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, biki ne mafi muhimmanci ga al’ummun kasar, Sinawa wadanda suka yi aiki har tsawon shekara daya su kan hadu da iyalansu a wannan gagarumin biki, amma yanzu domin rage hadarin yaduwar cutar COVID-19 sakamakon tafiye-tafiyen mutane, Sinawa da yawan gaske sun yi hakurin komawa garuruwansu, an yi hasashe cewa, fasinjojin dake tafiye-tafiye yayin bikin bazara na bana sun ragu da kaso sama da 60 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar 2019, kuma wani rahoton binciken da aka yi ya nuna cewa, ‘yan kwadago manoma fiye da kaso 77 cikin dari sun yi zabin yin murnar sabuwar shekara a wuraren da suke aiki.

Daga tafiye-tafiye zuwa yin murnar bikin a wurin aiki, an ga sauyin hanyar murnar bikin bazara ta al’ummun kasar Sin, lamarin shi ma ya nuna ingancin tsarin tafiyar da harkokin kasa na kasar Sin.

A gabannin bikin bazara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba zuwa lardin Guizhou domin rangadin aiki, inda ya taba ziyartar wata kasuwa a lardin domin kara fahimtar hakikanin yanayin da al’ummun kasar ke ciki, ta yadda za a tabbatar da samar da isassun kayayyakin da ake bukata yayin murnar bikin bazara da farashin da ya dace.

Bikin bazara na musamman ya nuna ingancin tsarin tafiyar da harkokin kasar Sin_fororder_2

Domin kara biyan bukatun mutanen da suke murnar bikin sabuwar shekara a wuraren da suke aiki, gwamnatin kasar Sin ta fitar da wasu manufofi, alal misali a birnin Beijing, fadar mulkin kasar, gwamnatin birnin ta bude lambunan shan iska ga masu yawon shakatawa ba tare da karbar kudi ba, kuma ta samar da takardun sayayya ta yanar gizo da takardun wasan kankara kyauta ga mazauna birnin, kana ta shirya ayyukan nishadantarwa iri daban daban yayin bikin bazara. A lardunan Zhejiang da Guangdong kuwa, gwamnatocin lardunan sun samar wa ‘yan kwadagon da suka zo lardunan daga sauran larduna kudi da rangwame da kudin sayen hidimar shiga yanar gizo ta wayar salula da sauransu, kamar yadda rahoton da aka wallafa a shafin yanar gizo na jaridar The Daily Telegraph ta kasar Birtaniya ta bayyana, an ce, daga kudin rangwame zuwa tikitin kallon fina-finai kyauta, gwamnatin kasar Sin tana kara karfafa al’ummun kasar gwiwa domin su yi murnar bikin bazara a wuraren da suke aiki.

Hakika bayan da kasar Sin ta jure wahalhalun da yaduwar cutar COVID-19 ta haifar, a bayyane an lura cewa, tsarin tafiyar da harkokin kasa na kasar Sin ya kyautata, har kullum gwamnatin kasar tana daukar matakan da suka dace yayin da take kokarin kandagarkin annobar, ana iya cewa, karfin gudanar da harkokin kasa na kasar Sin ya karu, matsayin gudanar da harkokin kasa na kasar ya dagu, duk wadannan sun burge al’ummomin kasa da kasa matuka, saboda an ga ko wanen Basine yana sauke nauyin dake wuyansa, kuma an ga wayewar kan daukacin zamantakewar al’ummar kasar ta samu ci gaba a bayyane.(Jamila)