logo

HAUSA

WHO Ta Musunta Zargin Da Aka Yiwa Kasar Sin Wai COVID-19 Ta Fito Ne Daga Wuhan

2021-02-14 19:16:33 CRI

WHO Ta Musunta Zargin Da Aka Yiwa Kasar Sin Wai COVID-19 Ta Fito Ne Daga Wuhan_fororder_0214-1

A kwanakin baya, an kammala binciken asalin kwayar cutar da ta haifar da annobar COVID-19 wanda tawagar hadin gwiwar kwararru ta hukumar lafiya ta duniyao WHO da kasar Sin suka gabatar, hukumar WHO ta gabatar da sakamakon bincike na farko, inda aka shaida cewa, cutar COVID-19 ba ta fito daga kasar Sin ba.

Tawagar kwararrun hukumar WHO ta kammala binciken asalin kwayar cutar COVID-19 har na tsawon kwanaki 28 a birnin Wuhan na kasar Sin, saidai ta bada bayani cewa, birnin Wuhan ba shine wurin asalin kwayar cutar ba, mai yiwuwa ne cutar ta shiga birnin ne ta hanyar dan Adam dake daukar cutar ko daskararrun dabbobin da aka shigar dasu zuwa kasuwar kayan teku ta Wuhan. Binciken ya bayyana cewa, kafin barkewar cutar COVID-19 a birnin Wuhan, an gano cutar a sauran kasashen duniya. Kana tawagar kwararrun ta tabbata cewa, Sin ba ta boye hakikanin gaskiyar lamarin ba.

Shugaban tawagar Peter Ben Embarek ya bayyana cewa, zargin da ake yiwa Wuhan na cewa kwayar cutar ta fito daga dakin gwaji na Wuhan ba shi da tushe, a nan gaba ba za a kara yin bincike kan wannan batu ba. Kana ya jaddada cewa, babu wani dakin gwaji a Wuhan dake da kwayar cutar, kuma babu wanda ya taba ganinta kafin barkewarta.

A yanzu dai, an musunta dukkan zargin da aka yiwa birnin Wuhan na kasar Sin na cewa cutar COVID-19 ta fito ne daga dakin gwaji na birnin. A shekarar 2020, cutar COVID-19 ta barke a dukkan duniya, A lokacin, ya kamata dukkan sassan duniya su yi hadin gwiwa don yaki da cutar, amma wasu kasashe suka yi amfani da cutar don cimma manufofinsu na siyasa, da zargi birnin Wuhan wanda aka gano cutar mai tsanani a karon farko a duniya a matsayin wajen da aka kyankyashe kwayar cutar. Jita-jita game da wannan batu ta barke a dukkan duniya a dogon lokaci, har ma wasu ‘yan siyasa sun ce wai birnin Wuhan na yin bincike kan cutar COVID-19, ko kuma cutar ta fito da hadari daga birnin. Amma a halin yanzu, bayan da tawagar kwararru ta hukumar WHO ta gama binciken a birnin, an musunta dukkan zargin da aka yiwa birnin Wuhan.

Hausawa su kan ce, gaskiya dokin karfe! Babu shakka gaskiya za ta fito a karshe, za a musunta dukkan zargin da aka yi ba tare da tushe ba, dukkan yunkurin da aka yi na yin amfani da jita-jita ko zargi ba zai cimma nasara ba.(Zainab Zhang)