logo

HAUSA

Murnar bikin bazara a wurin aiki ya nuna halin kishin kasa na Sinawa

2021-02-13 20:04:47 CRI

Murnar bikin bazara a wurin aiki ya nuna halin kishin kasa na Sinawa_fororder_11

Bikin bazara wato bikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, biki mafi muhimmanci ne na Sinawa, bisa al’adar kasar, ya dace Sinawa su koma garuruwansu domin haduwa da iyalai, amma yanzu ana kokarin kandagarkin yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a fadin duniya, Sinawa da dama suna murnar bikin a wuraren da suke aiki, bisa bukatar gwamnatin kasar, amma hakan bai rage soyayyar dake tsakanin al’ummun kasar ta Sin ba.

Alal misali, iyalai suna iya cin abinci tare ko taya juna murnar sabuwar shekara ta kafar bidiyo, kuma ana iya aika wa juna kayayyakin da ake bukata yayin murnar bikin ta yanar gizo, kana ana iya hada hotunan iyalai ta hanyar yin amfani da na’ura mai kwakwalwa, duk wadannan ba ma kawai sun samar da soyayya ta musamman ba, har ma sun samar da goyon baya mai karfi ga aikin kandagarkin annobar.

Alkaluman kididdigar da aka yi, kafin bikin bazara, sun nuna cewa,  adadin fasinjojin jiragen kasa da jiragen sama ya ragu bisa babban mataki idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, kuma a biranen kasar 36, manya ko matsaikaita, adadin mutanen da suka yi murnar bikin bazara a wuraren da suke aiki ya karu sama da miliyan 4.8 bisa bara.

Murnar bikin bazara a wurin aiki ya nuna halin kishin kasa na Sinawa_fororder_22

Sinawa su kan bayyana cewa, jarumai sun fito ne daga al’ummun kasa, a cikin shekara daya da ta gabata, wato tun bayan barkewar annobar COVID-19, al’ummun kasar Sin da yawansu ya kai biliyan 1.4 sun hada kai karkashin jagorancin gwamnatin kasar, har kokarinsu ya burge al’ummun kasa da kasa matuka. Yanzu haka al’ummun kasar Sin sun sake nuna wa al’ummun kasa da kasa halin kishin kasarsu ta hanyar daukar matakai, ciki har da murnar bikin bazara a wuraren da suke aiki, da haduwa ta yanar gizo da sauransu, kamar yadda babban mai ba da shawara ga babban jami’in hukumar lafiya ta duniya Bruce Aylward ya bayyana, ko wanen Basine na sauke nauyin dake wuyansa yayin da ake kandagarkin annobar.

Bana shekarar saniya ce bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, kuma bisa al’adar Sinawa, saniya na alamta kwazo da karfi, wadanda ke nunawa daga zabin Sinawa yayin da suke murnar bikin bazara. Duk da cewa, Sinawa da yawan gaske suna murnar bikin a wuraren da suke aiki, amma zukatunsu a hade suke, ko shakka babu kokarinsu zai ciyar da kasar Sin gaba yadda ya kamata.(Jamila)