logo

HAUSA

Gudummuwar Rigakafin COVID-19 Da Sin Ta Bayar Ta Taimaka Wa Afirka Wajen Yaki Da Cutar

2021-02-13 21:04:03 CRI

Gudummuwar Rigakafin COVID-19 Da Sin Ta Bayar Ta Taimaka Wa Afirka Wajen Yaki Da Cutar_fororder_微信图片_20210213210305

Wani bangare na allurar rigakafin COVID-19 da Sin ta bayar da gudummuwarta ga kasar Equatorial Guinea, ya isa Malabo, babban birnin kasar a ranar 10 ga wata, wanda ya kasance kashin farko na tallafin alluran rigakafi da gwamnatin Sin ta samar ga kasashen Afrika.Sa’an nan a ranar 11 ga wata, aka yi wa mataimakin shugaban kasar Teodoro Nguema Obiang Mangue allurar, wanda ya bayyana cewa, tallafin ya shaida ka’idojin hadin gwiwa da amfanawa al’ummar Afirka, wadanda Sin ke martabawa. Ban da wannan kuma, alluran COVID-19 dubu 200 da Sin ta bai wa kasar Zimbabwe za su isa kasar a ranar 15 ga wata.Shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya furta cewa, allurar ta kawo kyakkyawar makoma ga gwamnatinsa da jama’arsa wajen yaki da cutar, wadda ta yi kama da hasken da ke fitowa daga karshen dogon rami.

A halin yanzu ma dai, yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Afrika ya zarce miliyan 3.71. Daraktar hukumar WHO a Afrika Matshidiso Moeti, ta ce yawan mutanen nahiyar da suka mutu sakamakon cutar ya tsaya kan kaso 3.7, wanda kuma ya zarce matsakaicin adadin a duniya baki daya.Amma sabo da rashin ci gaban tattalin arziki da take da shi, gami da yadda kasashe masu sukuni ke sayen allurar da yawa fiye da bukatunsu, da wuya wasu kasashen Afirka ke iya samun allurar, balle ma gudanar da aikin yi wa al’umma allurar. Don haka, ana iya gano cewa, wadannan allurar COVID-19 da Sin ke tura wa Afirka, na daukar kaunar da Sin ke nunawa aminiyarta, haka kuma sun nuna yadda Sin ke cika alkwarinta na sa kaimi ga aikin rarraba allurar cikin adalci, da ma inganta hadin kan kasa da kasa wajen yaki da cutar.

Gudummuwar Rigakafin COVID-19 Da Sin Ta Bayar Ta Taimaka Wa Afirka Wajen Yaki Da Cutar_fororder_微信图片_20210213210316

Shugaban kasar Xi Jinping ya taba yin alkawari a yayin taron koli na musamman na hadin kan Sin da Afirka don yaki da cutar COVID-19, cewar bayan kasar Sin ta samu nasarar nazarin allurar rigakafin da ta fara amfani da su, to za su amfani kasashen Afirka da farko. Bugu da kari, ministan harkokin wajen kasar Wang Yi shi ma ya yi tsokaci bayan ya kammala ziyararsa a wasu kasashen Afirka hudu a farkon bana, cewar cutar COVID-19 na ci gaba da yaduwa a duk fadin duniya, Sin na son hadin kai da kasashen Afirka a fannin allurar rigakafin, ta yadda Afirka za ta iya samun allurar yadda ya kamata. Yanzu Sin na samar da allurar kyauta ga kasashe masu tasowa guda 13 ciki har da kasashen Afirka uku, wannan alama ce ta cika alkawarin da duniya ke bukata cikin gaggawa. Kamar yadda Jaridar NewYork Times ta kasar Amurka ta wallafa wani sharhin a kwanan nan, cewar ana sa ran ganin allurar COVID-19 ta kasar Sin ta zama dabarar ceton rayukan al’ummomin kasashe masu tasowa.

Bai kamata a ceci ran mutum bisa yawan kudin da yake da shi ba. Samar da taimako ga masu rauni gwargwadon karfi, da maida allurar COVID-19 a matsayin wani abun da kasashe masu tasowa ke iya saye, wani nau’in adalci ne da ya kamata a martaba. A ko da yaushe, Sin ba ta dakatar da takenta na raya makomar Sin da Afirka ta bai daya da makomar lafiyar bil adama ta bai daya.(Kande Gao daga sashen Hausa na CRI)