logo

HAUSA

An kori BBC daga kasuwar Sin bisa laifin karya dokar aiki

2021-02-12 20:01:17 CRI

An kori BBC daga kasuwar Sin bisa laifin karya dokar aiki_fororder_11

Yau Jumma’a, hukumar kula da harkokin kafofin watsa labarai ta kasar Sin NRTA, ta sanar da cewa, kafar watsa shirye-shirye ta kamfanin BBC mallakar kasar Birtaniya, ta karya dokokin aikin rediyo da talabijin, da dokoki masu nasaba da harkokin gudanar da shirye shirye kan tauraron dan Adam a ketare masu alaka da kasar ta Sin, wanda hakan ya sabawa sharadin wajibcin labarai ya kasance na gaskiya, da kaucewa son kai. Kaza lika hakan na yin kafar ungulu ga moriyar kasar Sin da ma hadin kan al’ummun ta. A don haka hukumar ta dakatar da kafar watsa shirye shirye ta BBC daga yada shirye shiryen ta a cikin kasar, bisa laifin karya dokar aiki, kana ba za ta amince da rokon yada shirye-shirye a kasar Sin a bana da ta gabatar ba.

Matakin kasar Sin ta dauka bisa doka, yana kiyaye ikon mulkin kasa da moriyar kasa, kuma yana kiyaye ka’idar wajibcin labarai ya kasance na gaskiya, yanzu haka an kori BBC daga kasuwar kasar Sin, sakamakon laifin da ta aikata.

BBC shahararriyar kafar watsa labarai ta kasashen yamma ce, wadda ta taba yada shirye-shiryenta a kasar Sin na dogon lokaci, shi ya sa ya kamata ta fahimci dokokin kasar Sin masu nasaba da hakan, amma abun bakin ciki shi ne, wannan shahararriyar kafar watsa labarai tana karya dokar aiki, duk da cewa ta san tana aikata laifin.

An kori BBC daga kasuwar Sin bisa laifin karya dokar aiki_fororder_22

A cikin watanni shida da suka gabata, tana yin kokarin yada jita-jita domin shafawa kasar Sin bakin fenti, duk wadannan sun nuna cewa, kafar watsa shirye-shirye ta BBC tana adawa da kasar Sin .

Hakika tun tuni an riga an gano cewa, kafar ta BBC tana gabatar da labaran kasa da kasa na karya.

Bisa matsayinta na shahararriyar kafar watsa labarai ta kasashen yamma, wadda ke da dogon tarihin shekaru 99, ko akwai bukata ta yi la’akari kan dalilin da ya sa aka kore ta daga kasuwar kasar Sin?

Kasar Sin tana samar da goyon baya da tallafi ga manema labaran kasa da kasa yayin da suke aiki a cikin kasar bisa doka, amma ba zai yiyu ta yi maraba da kafofin watsa labarai, wadanda ke zargin kasar Sin kamar yadda suke so ba.

Ya dace kafar yada shirye-shirye ta BBC, ta yi koyi da wannan darasi, ta nemi gafara daga kasar Sin bisa dalilin yada labarai na karya, amma idan ta ci gaba da yin adawa da kasar Sin, illar hakan za ta koma kanta.   (Jamila)