logo

HAUSA

Sin tana kara cimma manyan nasarori a fannin binciken sararin samaniya

2021-02-11 16:37:18 CRI

Sin tana kara cimma manyan nasarori a fannin binciken sararin samaniya_fororder_0211-2

A ranar Laraba 10 ga watan Faburairun nan ne, na’urar binciken duniyar Mars mai lakabin Tianwen-1 kirar kasar Sin, ta cimma nasarar shiga falakin duniyar Mars, wanda hakan ya kasance karon farko da kasar Sin ta kai ga nasarar shigar da wani kumbon bincikenta cikin wannan “Jar Duniya” kamar dai yadda ake yiwa duniyar Mars din lakabi da haka.

Masu aikin lura, tare da sarrafa wannan na’ura, sun ce ta kai ga shiga falakinta a duniyar ta Mars ne da karfe 8 saura mintuna 8 na almuru, bayan haye kalubale daban daban na fasaha.

Tianwen-1 ya zamo aikin sarrafa kumbuna, da na’urori daban daban da kasar Sin ta aiwatar cikin gwamman shekaru, yayin da kasar ke kara fadada ci gabanta a fannin binciken kimiyya da fasaha, da ayyukan sararin samaniya da na ’yan sama jannati.

A karo da dama, Sin ta sha harba kumbunan binciken samaniya masu dauke da ’yan sama jannati, da wadanda ke aiki ba tare da ’yan sama jannati ba.

Ana iya cewa, aikin da Tianwen-1 zai yi a duniyar Mars, zai zamo kari kan manyan nasarorin da Sin ta samu a wannan fanni na nazarin duniyoyin da ba na bil Adama ba. Wato kari kan aikace-aikace da aka cimma nasararsu, kamar na jerin kumbuna Beidou masu aikin samar da hidimar taswira, wanda kasar Sin ta fara cikin shekara ta 2000, ana kuma kammala harba rukunin taurarinsa a bara.

Kaza lika, aikin ya dada tabbatar da nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin amfani da rukunin rokar Long March, da aka rika amfani da su wajen harba taurarin bil Adama, da kumbuna, da sauran na’urorin binciken sararin samaniya.

Ko shakka babu, na’urar Tianwen-1, ta kafa tarihin zama irinta ta farko da kasar Sin ta harba, musamman domin binciken duniyar Mars, bayan harba ta daga tashar harba kumbuna ta Wenchang dake lardin Hainan a ranar 23 ta Yulin bara. Aikin da tuni ya kafa harsashin ci gaban kasar Sin, a fannin binciken duniyoyi daban daban baya ga duniyar bil Adama. (Saminu Alhassan)