logo

HAUSA

Tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugabanin Sin da Amurka ta nuna yunkurin kyautata alaka tsakanin kasashen biyu

2021-02-11 20:53:47 CRI

Tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugabanin Sin da Amurka ta nuna yunkurin kyautata alaka tsakanin kasashen biyu_fororder_1

Yau da safe dake zaman jajibirin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna da takwaransa na kasar Amurka Joseph R. Biden ta wayar tarho, inda suka taya juna murnar sabuwar shekara, suka kuma yi musayar ra’ayoyi mai zurfi kan alakar Sin da Amurka da manyan batutuwa dake shafar kasa da kasa da shiyya-shiyya, lamarin da ya jawo hankalin al’ummun kasa da kasa matuka. Hakika wannan ne karo na farko da shugabannin kasashen biyu suka tattauna ta wayar tarho tun bayan da sabuwar gwamnatin kasar Amurka ta fara rike mulki, inda sassan biyu suka fatan tattaunawar da suka yi ta wayar tarho za ta nuna wa al’ummun kasa da kasa yunkurinsu na kyautata alakar dake tsakaninsu.

A cikin tattaunawar da suka yi, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya waiwayi tarihin ci gaban huldar dake tsakanin Sin da Amurka a cikin shekaru sama da 50 da suka gabata, kuma ya sake jaddada cewa, hadin gwiwa shi ne zabi daya kacal dake gabansu. Shugaba Biden ya taba ziyartar kasar Sin har sau hudu, kuma ya fahimci yanayin da kasar Sin take ciki, a don haka ya taba nanata wajibcin gudanar da hadin gwiwa dake tsakanin Amurka da kasar Sin bayan da ya hau kan kujerar shugaban Amurka. A bayyane yake cewa, hulda mai inganci dake tsakanin Sin da Amurka ta dace da moriyar sassan biyu.

Tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugabanin Sin da Amurka ta nuna yunkurin kyautata alaka tsakanin kasashen biyu_fororder_2

A nasa bangaren, shugaba Biden ya bayyana cewa, ya kamata kasashen Sin da Amurka su guje wa hargitsi, haka kuma su gudanar da hadin gwiwa.

Abun farin ciki, gwamnatin Amurka ta nuna halin dattako yayin tattaunawar.

Kana yayin tattaunawarsu, shugaba Xi ya yi kira da cewa, ya dace sassan biyu wato Sin da Amurka su ba da gudummowa mai ma’anar tarihi a bangaren ingiza zaman lafiya da ci gaba na duniya.

Kafin wannan, shugaba Biden ya taba gabatar da wani rahoto game da manufar diplomsiyyar kasar, inda ya sanar da cewa, an farfado da diplomasiyya a Amurka, ana fatan Amurka za ta yi watsi da manufar bangaranci, kuma ta daina sanya moriyarta sama da komai, har ma ta sauke nauyin babbar kasa dake wuyanta, ta yi kokari tare da kasar Sin domin ciyar da duk duniya gaba yadda ya kamata.

Ana sa ran cewa, Amurka za ta cika alkawarin da ta yi, ta hada hannu da kasar Sin, ta yadda za su kyautata huldar dake tsakaninsu.(Jamila)