Zaman rayuwa mai dadi na kakani mata na kauyen Xunpu
2021-02-10 19:42:24 CRI
A birnin Quanzhou na kasar Sin, matan dake kauyen Xunpu sun shahara sosai a wurin, kuma suna da salon musamman na gyaran gashi da na kwalliya. Yawancinsu suna zaune ne a yankin Xunpu na gundumar Fengze dake birnin Quanzhou, wadanda kuma su zuriy’ar Larabawa ne a lokacin can can can da. Yanzu dai wasu kakanni mata dake kauyen Xunpu masu matsakaicin shekaru 70 sanye da kayan gargajiya suna rera waka, da rawa, da kuma gwaje-gwaje, sun shahara a yanar gizo. Gwaje-gwajen da suka yi irin na ‘yan kungiyar tsageru mata ne na wurin wanda aka yi a shekaru sama da goma da suka gabata.
Yawancin wadannan kakanni mata ta Xunpu sun taba shiga cikin kungiyar tsageru lokacin suna matasa. Kafin wannan, wani karamin bidiyo da aka dauka kan yadda suke samun horo irin na kungiyar tsageru ya samu karbuwa sosai a yanar gizo, inda ake iya gano cewa, ko da yake ba su kware sosai kan motsinsu ba saboda sun dade ba su samu horo ba, amma halin da suke nunawa yana da kyau da ban sha’awa sosai.
Wannan kungiyar na hade da mambobi 13, wadda ta fi tsufa shekarunta sun kai 78, kuma mafi kankantar shekaru ita ce mai shekara 63. Shugabar kungiyar Huang Liqing ta gaya mana cewa, a cikin ‘yan kwanakin nan, suna kokarin yin gwaje-gwaje, daga baya kuma, za su tsara wasan tsageru da raye-raye. A cewarta, yawancin mambobin dake cikin kungiyar sun taba zama ‘yan kungiyar tsageru, ita ma kanta ta kasance mamba a "aji mafi kwarewa" na kungiyar tsageru a lokacin da take matashiya. Yanzu shekaru sama da goma da suka gabata, tana iya tunanin yadda ake yin gwajin. Sauran kakanni mata kuma suna sha’awa tattauna yadda ake yin wasan tsageru da motsin raye-raye sosai.
Huang Liqing ta kara bayyana cewa, cikin shekaru 30 bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, ‘yan mata masu yawa na kauyen Xunpu sun taba shiga kungiyar tsageru. A lokacin, an kafa kungiyoyin aikin gona guda 14 a kauyen, an zabi mutane biyu ko uku daga ko wace kungiya domin ba su horo a fannonin harbe-harbe, yin gwaje-gwaje da dai sauransu. Saboda kauyen Xunpu yana fagen dake bakin ruwa na birnin Quanzhou, don haka akwai bukatar ‘yan kungiyar tsageru su tafi yin sintiri da dare, ‘yan kungiyar maza na daukar alhakin kai hari, mata na mai da hankali kan kare kai.
A sansanin nuna hotuna game da matan dake kauyen Xunpu, akwai wani tsohon hoto mai suna “‘Yan kungiyar tsageru mata na Xunpu ”,inda aka yi dauki yadda matan kauyen suke a wancan zamani, an kuma shaida halin jarunta na ‘yan kungiyar tsageru mata na kauyen. A cikin wannan hoton kuma, akwai wata mace mai suna Chen Jingchuan, a yayin da take waiwayen yadda suke aiki da zama a lokacin, ta gaya mana cewa, kullum suna gudanar da aikin gona da samun horo tare, su kan yi amfani da awoyi 20 a cikin kungiyar, inda sukan samu horo, da yin sintiri da kuma gasa. Da dare su yi barci a wani babban gado tare, kuma su kan yi gadi daya bayan daya, da bincike fitila dake jagora da gargadi don kada jirgi ya nutse. Kaka Chen Jingchuan ta gaya mana cewa, “Dole ne mutane uku su yi gadi tare, kamar yadda aka nuna a cikin wannan hoto.”
Bayan Chen Jingchuan ta yi aure, sai kungiyar tsageru ta mata ta watse sannu a hankali. Kamar yawancin matan dake kauyen Panpu, sun soma rayuwa ta hanyar kamun kifi. Ya zuwa yanzu dai, sun ajiye bindigoginsu, da ragar kamun kifin, kuma suna sanya kyawawan tufafi. A cikin lokacin hutu, suna taruwa, suna rera waka, da buga ganguna, da kuma yin rawa tare, sun soma wani irin zaman rayuwa mai dadi sosai. Game da wannan, kaka Chen Jingchuan ta ce,“Mu tsoffi ne, don haka mu kan manta da yadda motsin yake, amma ba damuwa, muna iya tattauna tare, wannan abu ne mai ban sha’awa. ”
Da ma wadannan kakani mata suna gudanar da ayyukansu ne a cikin al’ummarsu kadai, wadda ta sanya su shahara da samu karbuwa a yanar gizo, ita ce Huang Liyong, mai aikin yada al’adun gargajiya na kauyen Xunpu. An haife Huang Liyong a shekarar 1989 a kauyen na Xunpu. Tun da take yariniya ta fara sha’awar yin rawa da buga fiyano. A lokacin da shekarun haihuwarta suka kai 19, sai ta soma aikin gano da yada al’adun gargajiya na Xunpu, kana ta kafa sansanin nuna hotuna kan al’adun gargajiya na matan dake Xunpu, da nufin taimakawa kauyensu fita daga birnin Quanzhu zuwa kasar Sin har ma da duniya baki daya.
A shekaru biyu da suka gabata, Huang Liyong ta fara jagorantar wadannan kakani mata fita daga kauyen don halartar ayyuka daban daban, da fatan kara habaka al’adun gargajiya na Xunpu. Ta ce, ko da yake su toffi ne, amma a lokacin da suke kuruciya, dukansu suna kasancewa kamar maza, a cikinsu akwai malamai, da fitaciya a kungiyar tsageru dake kauyen. Duk da sun tsuffa, halinsu na himma da gwazo bai canja ba. Da ganin haka, sai Huang Liyong ta yi fatan shigar da salon ‘yan kungiyar tsageru mata a yayin da take tsara raye-raye da wakoki, ta hakan ake iya nuna halin musamman na Xunpu sosai.
Irin ra’ayin Huang Liyong ya samu amincewa daga wajen kakannin mata. Daga baya, sai ta dauki bidiyo kan yadda kakanin suke rera waka da halin zaman rayuwarsu mai kyau a yanar gizo, wadanda kuma suka samu karbuwa sosai daga masu kallon intanet.
A kwanan nan kuma, Huang Liyong ta sayo wasu kayayyakin amfani na wasan kwaikwayo, domin soma yin gwajin wasa irin na ‘yan kungiyar tsageru, kana tana kokarin tamakawa wadannan kakani mata rubuta wake-wake masu salon musamman na Xunpu. Kakani mata suna farin ciki da yin gwaji a ko wace rana, Huang Liyong ma tana kokarin ci gaba da daukar bidiyon kakanin. Muna cike da imanin cewa, “’Yan kungiyar tsageru kakanni mata”za su kasance wata alamar dake iya wakiltar al’adun Xunpu, ta yadda za a kara yada al’adun gargajiya ta Xunpu.