logo

HAUSA

Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ya Ingiza Hadin Kan Sin Da Kasashen Gabas Da Tsakiyar Nahiyar Turai

2021-02-10 11:17:45 CRI

Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ya Ingiza Hadin Kan Sin Da Kasashen Gabas Da Tsakiyar Nahiyar Turai_fororder_微信图片_20210210094923

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci taron koli na Sin da kasashen gabas da tsakiyar Turai wato taron China-CEEC ta kafar bidiyo a jiya Talata tare da ba da jawabi. Cikin jawabin, Xi Jinping  ya ba da shawarwari game da hadin kan Sin da kasashe 17 na wadannan yankuna, tare da gabatar da jerin muhimman matakai.

A cewarsa, sanin kowa ne, cikin dukkan dandamalin da Sin ta kafa, ci gaban wannan dandali na hadin kan Sin da kasashen gabas da tsakiyar Turai da aka kafa a shekarar 2012, ya fi jan hankalin mutane duk da cewa ba a dade da kafa shi ba.

Shugaba Xi ya ce, dandalin ya samu bunkasuwa mai kyau saboda dabaru guda 4, wato shawarwari da ake yi tsakanin mambobin da neman amfanawa juna da cin moriya tare, da kuma samun ci gaba ta hanyar bude kofa ga sauran kasashe da hakuri da juna, har ma da kirkire-kirkire ba tare da tsayawa ba da sauransu. Ya kara da cewa, ana iya ganin cewa, wadannan dabaru sun dace da manufar da Sin ta dade tana dauka na gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban da hadin kai da cin moriya tare. Shi ya sa, a ka kai ga cimma nasara a wannan fanni.

Shugaban ya ce a halin yanzu dai, Sin da wadannan kasashe na kokarin magance cutar COVID-19 da farfado da tattalin arizkinsu, don haka ana matukar bukatar hadin kai a tsakaninsu. Ya ce takardun hadin kai tsakanin gwamnatoci 35 da takardun hadin kai a fannin kasuwanci 53 da kuma jadawalin Beijing na hadin kan Sin da kasashen gabas da tsakiyar Turai na shekarar 2021, dukkansu, ci gaba ne da aka samu a cikin wannan gaggarumin dandali. (Amina Xu)