Na samu sauki sakamakon likitancin gargajiyar kasar Sin
2021-02-10 09:50:28 CRI
Jama’a masu sauraro, assalamu alaikum! Barkanku da war haka, barkanmu kuma da sake saduwa da ku a shirinmu na “Shekara Kwana”, wanda muka tsara musamman domin murnar cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Najeriya. Kuma ni ne Ibrahim Yaya a yau ke gabatar muku kashi na uku na jerin shirye-shiryen.
A cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku wani labari kan yadda wani asibitin, wato “Eastern and Western Hospital” da likitoci Sinawa biyu, wato Andy Yuan da matarsa Alisa suka kafa a Abuja, tarayyar jamhuriyar Najeriya. A lokacin da ya tabo dalilin da ya sa ya tsai da kudurin kafa wannan asibiti da yadda ’yan Najeriya, musamman ’yan arewan Najeriya suka taimake su a lokacin da suke shirya kafa asibitin, da gudanar da harkokin asibiti.