logo

HAUSA

Bayanan da aka fitar a taron da aka yi a Wuhan sun bata ran "masu ra'ayin makirci"

2021-02-10 22:19:30 CRI

Bayanan da aka fitar a taron da aka yi a Wuhan sun bata ran "masu ra'ayin makirci"_fororder_微信图片_20210210221738

A ranar 9 ga wata, a yayin taron manema labaru da hadin gwiwar tawagar kwararru ta kasar Sin da WHO kan nazarin asalin kwayar cutar annobar COVID-19 ta gudanar a birnin Wuhan na kasar Sin, shugaban tawagar a bangaren ketare Peter Ben Embarek ya bayyana cewa, maganar da aka yi wai cutar ta bulla ne daga dakin gwaje-gwaje, hakan “ba zai yiwu ba”, don haka, ba za a ci gaba da binciken asalin ta wannan hanya ba. Wannan sakamakon da aka samu ya kara wanke sunan cibiyar nazarin cututtuka ta Wuhan, wanda aka dade ana bata sunanta. A nasu bangaren, wadancan 'yan siyasa da kafofin watsa labarai na Amurka da na yammacin duniya da suka kirkiri wadannan makircin, ba za su ji dadi ba.

Ban da wannan kuma, game da bakin fenti da aka shafawa kasar Sin cewa, wai ta kawo cikas ga binciken da ake kan asalin cutar. A cikin kwanaki fiye da goma da suka wuce, mambobin tawagar kwararru na WTO da kasar Sin, sun yi nazari kan muhimman bayanai game da yaduwar annobar, sun kuma gudanar da bincike a hukumomi guda 9, ciki har da asibitin Jinyintan, kasuwar sayar da kayan teku ta Huanan, da cibiyar nazarin cututtuka ta Wuhan da dai sauransu, inda suka kuma tattauna da ma’aikatan lafiya, ma’aikatan cibiyar nazarin, masu aikin nazarin fasaha, jami’ai da ‘yan kasuwa, ma’aikatan al’umma, wadanda suka warke daga cutar, iyalan ma’aikatan lafiya da suka rasu sakamakon cutar, da kuma mazauna wurin da makamantansu.

Bayanan da aka fitar a taron da aka yi a Wuhan sun bata ran "masu ra'ayin makirci"_fororder_微信图片_20210210221748

Kamar yadda mamban tawagar a bangaren WHO Dr. Peter Daszak ya fada a yayin da yake zantawa da kafar yada labarai ta Bloomberg, “Mun ba da shawara kan inda za mu ziyarta, da kuma wadanda za mu tattauna da su. Mun yi bincike a duk wuraren da muka gabatar, mambobin tawagar a bangaren kasar Sin suna son kai mu wuraren sosai.”

Ana iya ganin cewa, a ko da yaushe kasar Sin tana gudanar da komai a bayyane game da binciken gano asalin cutar a duk duniya, kuma tana nuna goyon baya ga WHO wajen gudanar da ayyukan da suka dace, wanda ke nuna yadda babbar kasa dake sauke nauyin dake kanta. (Mai fassara: Bilkisu Xin)