logo

HAUSA

Ilimi hasken rayuwa

2021-02-10 15:11:30 CRI

Ilimi hasken rayuwa_fororder_A

A yau Laraba 10 ga watan Fabrairun shekarar 2021 ne, kasashen Sin da Najeriya ke bikin cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiya. A ranar 10 ga watan Fabrairun shekarar 1971 ne dai, kasashen biyu suka kulla dangantakar diflomasiya a tsakaninsu a hukumance, kuma tun wannan lokaci, kasashen suke zurfafa hadin gwiwa a fannoni daban-daban.

Ilimi wanda ke zama hasken rayuwa, na daya daga cikin bangagorin da kasashen biyu suke hadin gwiwa, kana daga guraben karo ilimi, da bude makarantun koyon harshen Sinanci a jihohin Najeriya da samar da kayayyakin koyo da koyarwa a Najeriya.

Bayanai na nuna cewa, yanzu haka akwai ‘yan Najeriya da dama wadanda suka ci gajiyar shirin guraben karo ilimi a jami’o’in kasar Sin daban-daban, matakin dake kara bayyana zurfin alakar sassan biyu.

A ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 2018 ma, gwamnatin kasar Sin ta ware Naira miliyan shida, don karrama wasu malaman makarantu da dalibai a Abuja, babban birnin kasar karkashin wani shirin gwamnatin kasar Sin na bunkasa harkar ilimi a tarayyar Najeriya. Kimanin makarantu 12 ne a Abuja suka ci gajiyar wannan shiri.

Ilimi hasken rayuwa_fororder_B

Shi ma ofishin jakadancin kasar Sin dake Najeriya, ya karrama wasu malamai da yawansu ya kai ashirin da hudu, da kayayyakin koyarwa don kara inganta kwarewa da kwazonsu na koyarwa. Haka su ma kamfanonin kasar ta Sin dake gudanar da harkokinsu a Najeriya, sun tallafawa daliban jami’o’i a Abuja, yayin bikin samun ’yancin kasashen biyu na ranar 1 ga watan Oktoba, duk wadannan na kara jaddada alakar kasashen biyu dake zama ’yan uwa kuma aminai na kwarai.

Mahukuntan kasar Sin dai, sun sha jaddada cewa, Ilimi shi ne muhimman makamin da kasar ta yi amfani da shi wajen kawar da al’ummarta daga kangin talauci, a don haka nema ta yi alkawarin ci gaba da bunkasa musata a wannan fanni tsakaninta da Najeriya, domin taimaka mata a kokarin da take na yaki da matsalar kangin talauci.

ilimi shi ke share fagen samun duk wani ci gaba, kana shi ke sauya fasalin tattalin arziki, baya ga yakar yanayin rashin jurewa juna, yana kuma taimakawa wajen kare duniyar mu, tare da cimma kudurorin ci gaba mai dorewa. Da fatan Sin da Najeriya, za su ci gaba da yaukaka alakarsu har zuwa badin badada. (Ibrahim)