logo

HAUSA

Ciki da gaskiya wuka ba ta huda shi

2021-02-09 15:23:26 CRI

Ciki da gaskiya wuka ba ta huda shi_fororder_微信图片_20210209152226

Asalin bullar cutar COVID-19 da ta addabi duniya cikin shekara guda da ta gabata, har yanzu abu ne da ake ci gaba da nazari kansa, wanda kuma ke ci gaba da jawo cece-kuce da nuna yatsa. Kasashen yammacin duniya, musammam Amurka na ta yada jita-jita ba tare da wata hujja ba cewa, cutar ta samo asali ne daga kasar Sin. Saboda kasar Sin ce kasa ta farko da ta sanar da bullar cutar a hukumance, ba zai taba tabbatar da cewa, a nan cutar ta samo asali ba ko kuma ita ta kirkiro ta ba. Ban da haka ma, nazarce-nazarcen da aka yi bayan bullar cutar, wanda kuma ake ci gaba da yi, sun nuna cewa an ga alamomin cutar a wasu kasashe tun ma kafin a kai ga gano ta a kasar Sin.

A kokarinta na binciken asalin cutar, kwararrun hukumar lafiya ta duniya WHO, sun ziyarci birnin Wuhan na kasar Sin, inda aka fara samun rahoton bullar cutar na farko a hukumance, kuma wanda a baya ya taba zama mafi fama da cutar. kuma ba tare da wani boye-boye ba, kasar Sin ta ba wadannan kwararru damar aiwatar da ayyukansu ba tare da wani shinge ko tsaiko ba. An kuma ba kwararrun damar ziyartar asibitocin da aka yi jinyar wadanda suka kamu da cutar, da kasuwar kayan ruwa da aka fara samun bullar cutar, har ma da tattaunawa da masu sayar da kayayyaki a kasuwar. Shin idan ita ce ta kirkiro cutar a dakin gwaji na birnin Wuhan kamar yadda jita jita ke cewa, za ta bari a shiga kasar har a je birnin da ma dakin gwajin don aiwatar da bincike? Wannan ba shi ne karon farko da jami’an hukumar lafiya ta duniya WHO suka ziyarci kasar Sin da birnin Wuhan dangane da cutar ba. Shin wace kasa ce ta bada wannan dama?

Babu wanda za a aminta da shi kamar bangare mai zaman kansa irin WHO da jami’anta wadanda ba Sinawa ba. Abun burgewa shi ne, yadda wadannan kwararru ’yan kasashen yammacin duniya suka tabbatarwa duniya shakkunsu dangane da zargin da ake cewa cutar ta samo asali daga kasar Sin.

Ciki da gaskiya wuka ba ta huda shi_fororder_微信图片_20210209152233

A cewar daya daga cikin kwararrun na WHO, Dokta Vladimir Dedkov, kwararre a fannin ilmin cututtuka masu yaduwa, kuma mataimakin shugaban cibiyar nazari na Pasteur da ke Saint Petersburg na kasar Rasha, kayayyakin dake dakin gwajin kwayoyin cuta na Wuhan suna da matukar inganci, kuma babu wanda zai iya fitar da wani abu daga cikinsa. Haka ma batun yake a bakin Peter Daszak, manazarcin dabbobi na kasar Birtaniya wanda ke cikin tawagar ta WHO.

Wannan na tabbatar da cewa babu wata shaida dake nuna cewa cutar ta samo asali daga dakin gwajin cututtuka na birnin Wuhan kamar yadda masu neman shafawa Sin bakin fenti ke ikirari.

Shi ya sa ya kamata a rika ajiye bambance-bambance ra’ayi a gefe kan batutuwan da suka shafi duniya. Wannan cutar ba ta ware wata kasa ko launin fata ko jinsi ba da ta tashi mamayar duniya. Ban da haka, ai kasar Sin za a iya cewa ta fi kowacce kasa shiga garari a lokacin da aka samu bullar cutar, duba da cewa, ta bulla ba zato ba tsammani, a lokacin da kasar ba ta da wata dabara ko hikima ta tunkararta. Don haka ta dauki tsauraran matakai kuma ta yi asarar dukiya da rayuka mai tarin yawa wajen tunkarar cutar. La’akari da wannan, ya isa hujjar cewa Sin ba ta kirkiro wannan cuta ba. Baya ga haka, duk wanda ya san tsarin shugabanci na gwamnatin kasar Sin, ya san cewa kasa ce da ta kan sanya bukatu ko muradun jama’arta sama da komai, a don haka, ba za ta taba kirkiro wani abu da zai sanya rayuwa da rayukan al’ummarta cikin matsanancin hali ba. Ban da haka, a kullum, ta kan ce makomar duniya a hade take, don haka, ta san cewa, duk wani abu da zai shafi al’ummar duniya, zai shafe ta, kuma a matsayinta na babbar kasa mai la’akari da sauran al’ummar duniya, ba za ta yi wani abu da zai kawo kalubale ga duniyar ba.

Zai kyautu, idan kasashen yamma dake yada wannan jita-jita, za su mayar da hankali wajen shawo kan cutar da ta dabaibaye su a yanzu, domin gujewa daukar nauyi da yada jita-jita ba za su amfana musu da komai ba, illa kara dagula al’amura. Sakamakon binciken WHO da hadin kan da Sin ta bayar, ya isa ya fahimtar da duniya manufar masu kin jinin kasar Sin. Kamar yadda a kan ce, ciki da gaskiya, wuka ba ta huda shi. (Faeza Mustapha)