logo

HAUSA

Masani: Kasar Sin ba za ta yi wa sauran kasashe zalunci ba

2021-02-09 14:11:01 CRI

Masani: Kasar Sin ba za ta yi wa sauran kasashe zalunci ba_fororder_2021-bayani-bello

Raul Sorrosa, shi ne wani shahararren masanin ilimin zaman al’umma, kana mai nazarin al’amuran siyasa, na kasar Ecuador. Ya gayawa wakilin babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG a kwanan baya cewa, kasar Sin ba za ta taba yi wa sauran kasashe zalunci ba, domin tana bin akidar hadin gwiwa tare da saura don tabbatar da moriyar kowa. Mista Raul Sorrosa ya ce, yana zumudin ganin fara taron shugabannin kasashen Sin da na gabas da tsakiyar nahiyar Turai. a cewarsa, a cikin shekarun da suka gabata, kasar Sin da kasashen gabas da tsakiyar Turai sun yi ta kokarin karfafa hadin gwiwarsu, inda manyan jami’an kasashen suka ziyarci juna a kai a kai, kana an yi kokarin gudanar da ayyuka masu alaka da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”. Game da hadin gwiwar kasashen a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da aikin ilimi, da al’adu, an samu nagartaccen sakamako, tare da kyautata tsare-tsarensu na hadin kai da juna. Sorrosa na ganin cewa, wani sako mai kyau da taron na wannan karo zai nuna wa duniya, shi ne wani ra’ayi na kin dunkulewar kasashe daban daban, da kokarin kare kai, gami da ta da yake-yaken ciniki, wanda ya taba yaduwa a duniya a lokacin da Donald Trump ke mulkin kasar Amurka, zai kai karshensa. A nata bangare, kasar Sin za ta iya taimakawa mai da kasashen Turai a matsayin cibiyar jigilar kayayyakin da aka samar da su a kasashe daban daban, don magance samun shingayen da za su hana jigilar kayayyaki. Kana kasar Sin ta nanata ra’ayinta na kasancewar bangarori masu fada a ji da yawa a duniya, da alkawarin da ta dauka na girmama mulkin kai na sauran kasashe, da rashin tsoma baki a harkokin cikin gidansu.

Yanzu haka, Mista Sorrosa yana zama a kasar Czekh, don haka shi ma ya yi tsokaci kan huldar dake tsakanin kasar Sin da kasar Czekh. A cewarsa, kasashen 2 za su kara kyautata huldar dake tsakaninsu a nan gaba. Sorrosa ya ce, kasar Sin ta riga ta zama wata babbar kasa mai karfin tattalin arziki, bayan da ta kwashe shekaru fiye da 40 tana kokarin aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida, da bude kofa ga kasashen waje. Don haka, ya kamata jama’ar Czekh su lura da muhimmancin kasar Sin. Da ma kasar Czekh na bukatar shigowa da dimbin kayayyaki daga sauran kasashe, kana ingantattun kayayyakin da ake samarwa a kasar na bukatar samun kasuwannin da za a rika sayar da su. Kana kasar Sin za ta iya biyan bukatun kasar Czekh daga dukkan fannonin guda 2. Misali, a shekarun baya bayan nan, an samu sayar da motocin samfurin Skoda kirar kasar Czekh da yawa zuwa kasar Sin. Ba domin kasuwannin kasar Sin ba, da tuni ma’aikata dubu 33 na kamfanin Skoda sun fuskanci matsalar rashin aikin yi. Kana yadda ake samun koma bayan tattalin arziki a kasar Czekh sakamakon annobar COVID-19 shi ma ya shaida muhimmacin masu yawon bude ido Sinawa ga sha’anin yawon shakatawa na kasar. A cewar Mista Sorrosa, kasar Sin aminiya ce, ba abokin gaba ba. Abun farin ciki shi ne, shugaban kasar Czekh Milos Zeman, da magabacinsa Vaclav Klaus, dukkansu suna son karfafa hadin gwiwa tare da kasar Sin. Ma iya cewa suna dora muhimmanci ne kan samun takamaiman ci gaba a kasarsu.

Ban da wannan kuma, Mista Sorrosa ya bayyana ra’ayinsa dangane da huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Latin Amurka. Ya ce, kasar Sin ba ta taba yin mulkin mallaka a yankin Latin Amurka ba. Tushen huldar kasashen yankin Latin Amurka da kasar Sin shi ne kokarin haifarwa juna da moriya. Saboda haka, Mista Sorrosa ya shawarici kasashen Latin Amurka da su kara kokarin hadin kai tare da kasar ta Sin, don neman samun karin ci gaban kasa.

Raul Sorrosa ya kara da cewa, zuwa yanzu kasar Sin ta zama kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya. Amma idan mun waiwayi yadda tattalin arzikin kasar yake wasu shekaru 50 da suka wuce, za a ga tattalin arzikin kasar bai kai na Mexico ko kuma Ecuador ba a lokacin. Ci gaban tattalin arziki da kasar Sin ta samu cikin wadannan shekaru 50, ya sa kasar ta zama wata babbar kasa dake taka rawar gani a al’amuran siyasa da tattalin arziki na kasa da kasa. Koda yake, har yanzu kasashen yammacin duniya na mai da dalar Amurka a matsayin ginshikin tsarin hada-hadar kudi ta duniya, amma za a iya kyautata zaton cewa kudin Sin RMB zai kara taka muhimmiyar rawa a duniya. (Bello Wang)

Bello