Shekarar Saniya na tafe
2021-02-09 18:23:16 CRI
Bisa kalandar gargajiya ta al'ummar Sinawa, wasu kwanaki suka rage, mu yi ban kwana da shekarar Bera, sai kuma mu fara shagulgulan sabuwar shekara ta Saniya.
Watakila kuna mamakin me ya sa ake cewa shekarar Bera, Zomo har da ta Saniya? A biyo mu cikin shirin Allah Daya Gari Bamban, don jin karin haske dangane da al'adar Sinawa ta kirga shekaru da dabbobi, inda muka samu damar tattaunawa tare da Dr. Bello Habeeb Galadanchi , wanda ya shafe wasu shekaru yana dalibta da kuma aiki a kasar Sin.(Lubabatu)