logo

HAUSA

Manufar masu ra’ayin yakin cacar baki ita ce sarrafa makomar huldar dake tsakanin Sin da Amurka

2021-02-08 21:45:08 CRI

Manufar masu ra’ayin yakin cacar baki ita ce sarrafa makomar huldar dake tsakanin Sin da Amurka_fororder_微信图片_20210208213835

Tun bayan da sabuwar gwamnatin Amurka ta kama mulki, kasashen Sin da Amurka su kan bayyana fatansu na yin hadin gwiwa, hakan ya sanya kasashen duniya suke sa ran ganin dawowar huldar da ke tsakanin Sin da Amurka kan madaidaiciyar hanya. Amma, a kwanan nan, wata fitacciyar hukumar masana ta Amurka ta fitar da wani rahoto, inda ta yi kokarin harzuka kiyayya a tsakanin kasashen biyu. Ban da wannan kuma, tsohon sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo shi ma ya ce manufar diplomasiyyar Biden za ta sanya “kasar Sin ta wulakanta Amurka”. Wani “mugun karfi" na gab da wucewa ta Washington, da nufin ingiza kasashen Sin da Amurka zuwa ga yin fito na fito

Wannan rahoton da ake kira "Sabbin dabaru bisa manyan tsare-tsare kan kasar Sin" ya tattaro maganganun da gwamnatin Amurka da ta gabata ta aikawa kasar Sin, ya kuma yada "barazanar da kasar Sin ke kawowa", ya kuma ce, wai babbar manufar hana kasar Sin ita ce kiyaye matsayin mallaka na Amurka, kana kuma ya bayyana manufar dabaru bisa manyan tsare-tsare kan kasar Sin da kuma shirin aiwatarwa.

Manufar masu ra’ayin yakin cacar baki ita ce sarrafa makomar huldar dake tsakanin Sin da Amurka_fororder_微信图片_20210208213828

An zabi lokacin da sabuwar gwamnatin Amurka ta fara aiki don gabatar da wannan rahoton, ta haka ake iya gano makasudin sace manufofin Amurka game da kasar Sin. Mujallar National Interest ta Amurka ta yi sharhi cewa, akwai kuskure a cikin rahoton game da manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen Sin da Amurka.

A lokaci guda kuma, tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya fada kwanan nan cewa, manufar diplomasiyya ta gwamnatin Biden za ta sanya "kasar Sin ta wulakanta mu." Game da wannan mummunan nufin na lalata hadin gwiwa a tsakanin Sin da Amurka don amfanin kansa, masu amfani da yanar gizo sun ce: "Pompeo ya yi tunanin zai zama dan takarar shugaban kasa, amma abin dariya ne kawai."

An lura cewa, sabuwar gwamnatin Amurka ta sha nuna aniyarta ta yin hadin gwiwa da kasar Sin, kuma ana sa ran dangantakar Sin da Amurka za ta bude sabon babi. Ana fatan ganin, sabuwar gwamnatin Amurka za ta nuna gaskiya da sahihanci don yin kokari tare da kasar Sin da nufin kyautata dangantakar dake tsakaninsu. (Bilkisu Xin)