logo

HAUSA

Shekara kwana: Sin da Najeriya na cika shekaru 50 da kulla zumunci

2021-02-08 16:49:57 CRI

Shekara kwana: Sin da Najeriya na cika shekaru 50 da kulla zumunci_fororder_A

Masu hikimar magana na cewa “shekara kwana ce.” Tun bayan da gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin ta kaddamar da manufarta na yin gyare gyare a gida da kara bude kofarta ga katare a shekarun 1978, batun kyautata hulda a tsakanin kasar da sauran kasashen duniya na daya daga cikin muhimman ajandodi da mahukuntan kasar Sin suka sanya gaba domin karfafa cudanya da kasashen duniya. A ranar 10 ga watan Fabrairun shekarar 1971 ne Sin da Najeriya suka aza tubalin gina huldar diflomasiyya a hukumance a tsakaninsu. Bisa lura da yadda alakar dake tsakanin kasashen ke cigaba da karfafuwa, musamman duba da yadda ake samun bunkasar hadin gwiwar cinikayya da tattalin arziki a tsakanin kasashen, gami da alaka tsakanin mutum da mutum na al’ummun kasashen biyu, za a iya cewa kwalliya tana biyan kudin sabulu. Masu salon magana su kan ce, “Na ji dadi shi ne gari ba nasaba ba.” Bisa la’akarin da zumunci mai karfi da cudanyar dake tsakanin kasashen biyu, jama’a daga bangarori daban daban da suka hada da masana, ’yan kasuwa, har ma da jami’an gwamnatoci na kasashen biyu suna ci gaba da tofa albarkacin bakinsu game da cika shekaru 50 da kafuwar huldar kasashen biyu. Alal misali, a farkon wannan mako, ministan harkokin wajen Najeriya ya ce kasarsa tana koyi da irin salon dabarun kasar Sin wajen bunkasa tattalin arzikinta. Geoffrey Onyeama, ya ce Najeriya tana koyi da kasar Sin domin cimma nasarar bunkasa tattalin arzikinta da kuma rage dogaro kan kayayyakin kasashen ketare. Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci game da cika shekaru 50 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, Onyeama, ya fadawa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa, Najeriyar tana kan hanya mai bullewa yayin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sa himma tare da bada dukkan fifiko wajen bunkasa tattalin arzikin kasar, musamman fannin aikin gona. Ya kara da cewa, "Za mu yi koyi daga irin salon dabarun da gwamnatin kasar Sin ta aiwatar." A cewarsa, wadata al’ummar kasa da abinci shi ne babban ginshiki kuma tushen cigaban kasa, kuma kasar Sin ta samu manyan nasarorinta ne tun daga tushe ta hanyar bunkasa fannin noma.

Shekara kwana: Sin da Najeriya na cika shekaru 50 da kulla zumunci_fororder_B

Wannan shi ne dalilin da yasa shugaba Buhari ya bada fifiko a fannin bunkasa aikin gona domin Najeriyar ta samu damar tsayawa da kafafunta don wadata al’ummar kasar da abinci, da samar da guraben aikin yi, da samun yalwar arziki da wadata. Ko shakka babu, kasar Sin ta kasance tamkar madubi ce ga Najeriya, da ma dai an ce, “daga na gaba ake iya gane zurfin ruwa.” (Ahmad Fagam)