logo

HAUSA

Shirye shiryen gasar Olympic ya samar da damar bunkasa wasannin hunturu

2021-02-07 10:25:32 CRI

Shirye shiryen gasar Olympic ya samar da damar bunkasa wasannin hunturu_fororder_20190917083306877

Damar shirya gasar Olympics da birnin Beijing zai karbi bakunci lokacin hunturu da gasar Olympics ta nakasassu, ta kara fito da karfin kasar Sin a fannin kyautata wasannin kankara, kaza lika masu sha’awar wasannin kankara da na dusar kankara su ma sun samu karin fifikon inganta wasannin su.

Yanzu haka masu sha’awar wannan fanni na wasanni na samun karin karsashi, yayin da kamfanoni dake aiki a fannin ke kara fadada harkokin su. Tuni kuma kudurin sanya mutane kimanin miliyan 300 shiga harkokin wasan kankara ya fara cimma nasara.

A farkon shekarar nan, an samu yaduwar labarai masu dadi cikin sauri. Daga Laiyuan na lardin Hebei, zuwa tsaunin Changbai na lardin Jilin. Kai har da ma Jizhou na birnin Tianjin, Sinawa na shiga wasannin kankara tare da kara kwarewa, da cimma manyan nasarori a sassan wasan daban daban. Rahotanni sun nuna yadda daidaikun ‘yan wasa suka kafa tarihin bajimta mai gamsarwa, inda har aka samu wadanda suka nuna fasahohi koli da aka gani a wasu lokuta, tsakanin manyan ‘yan wasa na kasa da kasa, yayin da kuma wasu suka karya matsayin bajimtar wasan na cikin gida.

A shekarar nan ta 2021, shirin da ake yi na tunkarar gasar Olympic ta lokacin hunturu, ya kai wani muhimmin matsayi a tarihi. An yi kyakkyawan shiri, an kuma cimma nasarori. Yanzu haka dukkanin wuraren da za a gudanar da gasar an kammala su, a hannu guda kuma an tsara gudanar da horo a matakai daban daban ga ‘yan wasa yadda ya kamata.

Yanzu haka harkar wasannin kankara ta kankama, daga "yankin wasan kankara na Arewaci zuwa na kudu, da yammaci zuwa na gabas", duk suna dauke da halaye na musamman na wasannin da za a iya yi lokacin hunturu da wasu na lokacin bazara, cike da kankara da dusar kankara mai taushi.

Shirin gasar wasannin Olympic ya kai wani muhimmin mataki

A ranar 2 ga watan Janairu, Song Qiwu dake cikin tawagar masu samun horo, karkashin hukumar kasar Sin mai lura da wasan zamiyar kankara na tsalle, ya zamo na farko cikin ‘yan wasan Sin da ya kai ga yin tsallen da ya kai mita 140, a filin cibiyar bincike da horaswa ta wasan kankara dake Laiyuan.

Can a tsaunin Changbai kuwa, a filin wasan kankara na Wanda, Su Yiming ya yi nasarar tsalle da juyawa baya da ya kai digiri 1800 a waje, a tsawon makwanni 5 na gudanar da horo. Wannan ne kuma karon farko da wani dan wasan kasar Sin ya kafa wannan tarihi na bajimta a fannin wasan kankara.

A yayin gasar Olympic ta shekarar 2018 a Pyeongchang, tawagar ‘yan wasan Sin sun shiga takara a wasanni kanana har 55. Ana iya cewa, shirin tawagar Sin a yanzu, ya dara ta lokacin baya daga matakin kwazo zuwa mai matukar kwazo, kana kuma wuraren da ‘yan wasa ke samun horo sun karu zuwa wurare da dama gwargwadon bukatar da ake da ita, yayin gasar birnin Beijing dake tafe. Yanzu haka ‘yan wasa na tawagogin wasannin rukuni daban daban na Sin sun kara himmar horo, da kirkiro sabbin dabarun zama cikin shiri, sun kara shigar da binciken kimiyya, da riko da ka’idojin kimiyya da fasaha, tare da fadada dukkanin sassan shiri.

A lokaci guda kuma, an fadada karfin gwiwa na gargajiya na karfafa shirin tawagogin. A ranar 3 ga watan nan na Janairu, an gudanar da wasan tseren allon zamiya na mita 1500 zangon wasan kusa da kusan na karshe, na shekarar 2020 zuwa 2021 a birnin Tianjin.

Dan wasa Zhu Yiyue mai shekaru 18 da haihuwa ne ya zamo a kan gaba, inda ya lashe zangon gasar, ya kuma karya matsayin bajimtar da aka kafa a baya, bayan kammala zamiyar cikin mintuna 2, da dakika 9.257. Wanda hakan ya sanya shi zama na uku a jerin ‘yan wasa mafiya kwarewa a fannin zamiyar kankara ta wannan rukuni.

Ana dai danganta wadannan nasarori ne da tallafin da fannin kimiyya ke bayarwa ga inganta harkokin wasa. Tun daga bangaren yin horo, da samar da dakunan binciken harkokin wasanni, da nau’oin kayan da ‘yan wasa da ake amfani da su, da kuma sauran kayan da ake bukata a wuraren wasan. Kusan a iya cewa, fasahohi sun riga sun ratsa daukacin sassa na shirin da ake yi don tunkarar gasar Olympic ta lokacin hunturu a nan kasar Sin.

A cewar Ni Huizhong, daraktan wasanni a hukumar lura da shirya gasar dake tafe "Wadannan matakai sun ba mu damar bullo da dabaru, yanzu ba “lalube cikin duhu”, muna iya karya matsayin bajimta, muna kirkire kirkire a fannin horaswa. A hankali za mu wuce gaba a wasu fannoni, ta yadda za mu zamo masu fifiko a bangaren wasannin zamiya, da sauran wasanni masu nasaba da kankara."

Wasannin kankara da na dusar kankara na azurta mutane

A lokacin tsakiyar hunturu, filin wasan zamiya yana zama cike da masu sha’awar wasan, idan an kwatanta da sauran lokuta na shekara. A shekarun baya bayan nan, an gina karin irin wadannan wurare a sassa da dama na kasar Sin, wadanda suka zama zabin mutane da yawa a fannin zuwa shakatawa da hutu.

Domin yayata wannan fanni na wasanni, Sin ta aiwatar da wani shiri na fadada yankunan kudanci, da na yammaci da na gabashi na wannan wasa. Tun daga shekarar 2015 zuwa 2019, adadin wuraren da ake wasan zamiyar kankara sun karu daga 157 zuwa 388, kana manyan wuraren shakatawa dake kunshe da filayen wasan kankara sun karu daga 568 zuwa 770. A daya bangaren kuma, an fadada samar da abubuwan bukata na gudanar da wasan, kamar bunkasa samar da kankara da dusar kankara a wuraren da ake bukatar su.

A biranen Changchun, da Jilin, zango na 7 na lokacin shiga wasannin kankara da dusar kankara na kasa, ya baiwa al’umma damar sauyawa daga masu tsoron yanayin sanyi, zuwa masu shiga wasannin kankara.

Ana iya ganin masu sha’awar wasan kankara na kai-komo daga tudu zuwa gangaren filayen wasan. Akwai kuma wurare da aka tanada zomin tsere a titunan musamman da aka tanada, masu gajeren zango, ga kuma masu ba da horo da ‘yan kallo da yawa, kuma ana iya jin shewar ‘yan kallo a lokutan da kwararru a wasan ke nuna fasahohi masu birge kowa.

A birnin Shanghai, an bude wasan kasa na watanni 3, wanda shi ma ya baiwa al’ummar kasar damar yin nishadi da more rayuwar su ta wasannin kankara. Ana dai shirya zagaye zagaye na gasannin nau’oin wasannin kankara daban daban, ana kuma nuna fasahohi masu kayatarwa dake matukar jan hankalin masu kallo. A birnin Altay na jihar Xinjiang, an kaiwa wani bangare na darussan motsa jiki ga dalibai zuwa wurin wasan zamiyar kankara dake yankin. Tun daga watan Nuwamban shekarar 2020 da ta gabata zuwa watan Janairun 2021, wasu makarantun firamare da na sakandare 5, sun samar da darussan koyon zamiyar kankara a ko wane yammaci ga daliban su, ta yadda yara kanana za su kara sha’awar su ga wasan, tare da fadada raya al’adu da wasanni a rayuwar su a makaranta.

Jan hankalin Sinawa da yawan su ya kai miliyan 300 shiga wasannin kankara, muhimmin kuduri ne da Beijing ta sanya gaba, lokacin da birnin ya shiga hadin gwiwa da birnin Zhangjiakou, a yunkurin sa na neman izinin karbar bakuncin gasar wasannin Olympics ta hunturun 2022.

A yanzu haka, duk shekara, kasar Sin na aiwatar da ayyukan da suka shafi wasannin kankara, da dusar kankara na al’umma masu yawa sama da sau 3,000. Wasannin kankara da dusar kankara sun riga sun zamewa Sinawa da dama jiki. Yanzu dai ana daf da cimma burin da kasar ta tsara shekaru 5 da suka gabata.

Masana’antun wasannin kankara da dusar kankara na kara samun ci gaba

A ranar 30 ga watan Disambar bara ne aka gudanar bikin bude layin dogo na jirage masu saurin tafiya tsakanin biranen Beijing zuwa Zhangjiakou. A shekarun baya bayan nan, wannan layin godo na Beijing zuwa Zhangjiakou, ya yi jigilar fasinjoji sama da mutane miliyan 6.8. Ana iya ganin "Abokan kankara" sanye da kayan wasan, da allunan zamiya cikin fasinjojin dake bin wannan layin doga.

Daga tsakiyar watan Nuwamba zuwa farkon watan Disambar 2020, yawan masu zuwa wasan zamiyar kankara ya karu da kaso 20% zuwa 30%, inda jimillar masu ziyartar filayen wasan ya kai mutum 170,000 kamar yadda Huang Mengxin, mataimakin babban manajan filin wasan kankara na Wanlong Ski Resort dake Chongli, a lardin Hebei ya bayyana.

A cewar Wu Bin, mataimakin shugaban kungiyar masu wasan kankara na birnin Beijing, filayen wasa da aka kyautata, da layukan dogo da aka samar, sun kara inganta shirin kasar Sin na bunkasa wasannin kankara. Kaza lika karkashin tanadin matakan kandagarkin barkewar annobar COVID-19, da shawo kan cutar, masu yawon shakatawa dake ziyartar wadannan filaye sun fara komawa ziyartar wuraren, wanda hakan ke nuni ga ingancin shirin da aka yi.

Zhao Yuxuan matashiya ce mai shekaru 23 da haihuwa, wadda ke aiki a birnin Beijing, ta kuma shafe shekarun baya bayan nan tana yin wasan kankara. Zhao ya gudanar da wasan a filayen dake Chongli, da Hebei, da Daxing da yankin Fengtai dake Beijing. A cewar ta "Na kan fita wasa a karshen mako, Amma lokaci ne mai yawan jama’a. Manya da kanana suna nishadi." Zhao Yuxuan ta ce har yanzu tana matakin farko ne na koyon zamiyar kankara, kuma ba ta kai ga sayen kayan wasan na kashin kan ta ba. Tana kashe kudi ne kawai a sayen tikiti da lokacin shiga wasa.

Domin rage tsadar kudin shiga wasa, da yawa daga masu shiga wasan na hada kudi su shiga tawaga daya, don cin gajiyar rangwame.

A Huang Mengxin, mataimakin babban manajan filin wasan kankara na Wanlong Ski Resort dake Chongli a lardin Hebei, ya ce a baya, masu sha’awar wasan kan so su yi yini daya da rabi a filin, amma yanzu ana samun masu zuwa don yin rabin yini kadai. Huang na cewa "Hakan ya nuna yadda wasan kankara ke kara fadada a Sin, kuma adadin masu shigar sa ke karuwa, musamman ma masu koyon wasan a matakin farko.

Huang ya kara da cewa, idan an kalli wadannan alkaluma, za a ga kudaden da masu samun horo a filin Wanlong Ski Resort ke samarwa sun ninka na baya cikin shekaru 2 a jere.

A ta bakin Wu Bin, mataimakin shugaban kungiyar masu wasan kankara na birnin Beijing, shekarar nan ta 2021, ita ce ta farko cikin shekarun aiwatar da manufar raya kasar Sin karo na 14. Kuma domin kara bunkasa fannin wasannin motsa jiki ta yadda zai zamo ginshikin raya tattalin arzikin Sin, an tsara mayar da wasannin kankara daya daga ginshikan cimma wannan buri. A daya bangaren kuma, manufar nan ta zaburar da Sinawa miliyan 300 su shiga wasannin kankara da dusar kankara, ita ma tana taimakawa matuka. Ana sa ran nan gaba kadan, wannan masana’anta za ta cimma dukkanin nasarori, kana nan da shekaru 3 zuwa 5, za a ga babban sauyi a fannin wasannin hunturu a nan kasar Sin.